'Yan Bindga Sun Kai Hari a Zamfara, an Yi Awon Gaba da Mata da Yara
- ’Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a wani kauyen jihar Zamfara inda su ka tafka ta'asa
- 'Yan bindigan sun yi kisa tare da yin awon gaba da mutane kusan 20, da su ka hada da mata da kananan yara
- Sojojin da ke makwabtaka da wurin sun kasa kai daukin gaggawa saboda rashin ababen hawan da za su isar da su zuwa kauyen
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Mutum daya ya rasa rayuwarsa yayin da ’yan bindiga su ka kai wani hari a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun kuma sace mata da yara 18 a harin wanda suka kai a kauyen Birnin Zarma da safiyar ranar Juma’a.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
Jaridar The Punch ta ce wani mazaunin kauyen, Ibrahim Bello, ya ce ’yan bindigan sun farmaki kauyen ne da misalin karfe 5:00 na safe, lokacin da jama’a ke shirin fita sallar asuba.

Kara karanta wannan
An bankado abubuwa, matar shedanin 'dan bindiga ta shiga hannu a Zamfara, ta tsure
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sun kutsa wani gida, su ka kashe wani manomi mai suna Garba Gambo, su ka raunata matarsa da bindiga, sannan suka yi awon gaba da mata da yara 18 daga kauyen."
- Ibrahim Bello
Wani mazaunin garin Bukkuyum, Lawal Umar, ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa ’yan bindigan sun fito ne daga dajin da ke kusa a karamar hukumar Anka, inda suke da sansanoni.
Sojoji sun kasa kai dauki
Ya ce duk da akwai sojoji a Bukkuyum don hana farmaki, ba su iya isa wurin ba saboda kogin da ke tsakanin Bukkuyum da Birnin Zarma ya cika da ruwa, babu kuma jiragen ruwa don tsallakawa su.
Har yanzu mutanen Kauyen Birnin Zarma, wanda ke da tazarar kilomita 170 daga Gusau, babban birnin jihar, na jiran ko ’yan bindigan za su fito da bukatar neman kudin fansa.
A karshen watan da ya gabata, fasinjoji 15 mafi yawansu mata da yara, sun nutse a cikin ruwa bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife a kan hanya yayin da suke gujewa harin ’yan bindiga a kauyuka uku na karamar hukumar Gummi ta Zamfara.

Source: Original
Rashin tsaro ya zama ruwan dare
Wani mazaunin Zamfara, Jamilu Abdullahi, ya shaidawa Legit Hausa cewa matsalar rashin tsaro ta zama ruwan dare.
"Lamarin sai dai Allah ya kyauta kawai domin a kusan kullum sai an kai hare-hare a wasu yankunan jihar nan."
"Sai dai adduar Allah ya kawo mana saukin wannan fitinar."
- Jamilu Abdullahi
Karanta karin wasu labaran kan 'yan bindiga
- Dubu ta cika: An kama 'yan bindigan da suka kai hari masallaci ana sallar asuba
- Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka
- Al'umma sun samu sauƙi, ƴan bindiga sun hallaka rikakken ɗan ta'adda da yaransa 4
- An zo wajen: Gwamna Dauda ya yi fallasa kan matsalar 'yan bindiga a Zamfara
'Yan ta'adda sun yi ta'asa a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun yi basaja wajen tsula tsiya a jihar Zamfara.
'Yan ta'addan sun badda kama inda su ka farmaki garin Dansadau da ke karamar hukumar Maru ta jihar, da sassafe lokacin da wasu mutanen ke tsaka da barci.
Miyagun wadanda su ka sanya hijabai da rigunan mama, sun yi awon gaba da mutum takwas wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

