Sarki Sanusi II Ya Fadi Bala’in da Za a Shiga da Tinubu Bai Cire Tallafin Mai ba

Sarki Sanusi II Ya Fadi Bala’in da Za a Shiga da Tinubu Bai Cire Tallafin Mai ba

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana an yadda ake samun lalatattun shugabanni a Najeriya
  • Basaraken ya ce kasar ta dade tana fama da shugabanni marasa inganci, lamarin da ya hana cigaba sosai
  • Sanusi II ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ya ceci kasar daga durkushewa, yana mai ba matasa shawara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa game da irin kalar shugabanni da Najeriya ke samu tun da jimawa.

Sarki Sanusi II ya bayyana cewa Najeriya ba ta yi sa’a da shugabanni masu nagarta ba na dogon lokaci.

Sanusi II ya ba matasa shawara kan shugabanci
Sarki Kano, Muhammadu Sanusi II a fadarsa. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Twitter

Sanusi II ya koka kan shugabanci a Najeriya

Rahoton Daily Trust ya ce basaraken ya bayyana haka ne a Kano a jiya Asabar 13 ga watan Satumbar 2025 yayin taron cibiyar KAPFEST.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari ya rufe iyakoki, Tinubu ya bude su domin karya farashin abinci

Ya ce kasar ta sha fama da shugabanni “marasa amfani” na shekaru da dama, abin da ya haifar da durkushewar shugabanci da rikice-rikice.

Sanusi II ya kuma yi gargadi cewa kasar da ta ci gaba da samun irin waɗannan shugabanni ba za ta taɓa samun ci gaba mai ma’ana ba.

A cewarsa:

“Kasashen duniya suna tattauna cigaban fasaha da yanayi, mu kuma muna makale cikin maganar kabilanci da addini.”
Sanusi II ya koka kan shugabanci a Najeriya
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a cikin fadarsa da ke birin Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Twitter

Shawarar Sanusi II ga matasa a Najeriya

Sanusi II ya ce ana bata lokaci a majalisu da muhawarori marasa amfani, maimakon tattaunawa kan muhimman abubuwa da za su inganta rayuwa.

Ya bukaci matasa su farka daga barci su karɓi shugabanci, tare da cewa da himma za su iya kawar da tsofaffi daga mulki, Punch ta ruwaito.

Menene Sanusi ya ce kan cire tallafin mai?

Sanusi II ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ba abu ne da za a yi siyasa da shi ba, domin ya ceci Najeriya daga karyewa.

Kara karanta wannan

NNPCL: Mele Kyari ya yi magana bayan EFCC ta masa tambayoyi kan almundahana

“Tallafin da ake biya kawai muna bai wa Turai aiki ne, muna tallafa musu maimakon masana’antar mu ta cikin gida ta amfana.”

- Cewar Sanusi II

Sanusi II ya kara da cewa idan tun 2012 aka bi shawarar cire tallafin, da Najeriya ta fi samun sauƙi a tattalin arzikinta a yanzu.

Ya bayyana damuwa kan yadda gwamnati ke ci gaba da cin bashi da kashe shi ba bisa ka’ida ba, abin da zai shafi tattalin arziki.

Tun da farko, Daraktar PWI, Nasiba Babale, ta bayyana cewa KAPFEST na wannan shekara ya maida hankali ne kan waka a lokacin rikici.

Ta ce burin taron shi ne tunatar da mawaka da masu fasaha yadda za su yi amfani da zane da waka wajen yada zaman lafiya.

PhD: Masarautar Kano ta taya Sanusi II murna

Kun ji cewa jami'ar SOAS da ke birnin Landan ta yaye Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II bayan kammala digiri na uku.

Masarautar Kano ta fitar da sakon taya murna ga Mai Martaba Sarki Sanusi II bisa wannan nasara da ya samu a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu da kansa ya fadi abubuwan da ya tattauna da shugaban Kasar Faransa

Tawagar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ta je Landan domin halartar bikin yaye Sanusi II wanda ya karbi shaidar digirin digirgir.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.