Maganar N Power Ta Dawo, Abba Hikima, Ɗan Bello Za Su Koma Kotu da Gwamnatin Tinubu
- Lauya Abba Hikima da abokin gwagwarmarya sun shirya daukar mataki kan gwamnatin Bola Tinubu a Najeria
- Abba Hikima da Dan Bello suka ce za su koma kotu domin ci gaba da shari’a kan kuɗin N-Power da aka daina biya
- Sun bayyana cewa minista jin kai ya ce tun watan Yuli za a biya, amma har yanzu babu wani abin da gwamnati ta yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An dawo da maganar basukan matasa da suka ci gajiyar shirin N-Power da aka fara tun daga gwamnatin Muhammadu Buhari.
Majiyoyi sun bayyana cewa shari’a kan kudin N-Power da ake bin gwamnati za ta ci gaba bayan shafe watanni ba tare da biya ba.

Source: Facebook
N-Power: Hikima, Dan Bello za su koma kotu
Dan gwagwarmaya, Dan Bello shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 13 ga watan Satumbar 2025 a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin dan gwagwarmaya ya ce da shi da lauya mai kare hakki, Barrista Abba Hikima, da abokan gwagwarmayarsa suna shirin komawa kotu.
’Yan gwagwarmayar sun ce za su ci gaba da shari’ar a ƙarshen watan Satumba bayan kotuna sun dawo daga hutu, sakamakon alkawuran karya daga Ma’aikatar Harkokin Jinƙai.
A cewarsu, Ministan Harkokin Jinƙai a lokacin, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya tabbatar tun watan Yuli cewa an shirya biyan masu amfana, amma har yanzu babu wani abu.

Source: Facebook
Shirin yan gwagwarmaya kan basukan N-Power
Sun bayyana cewa duk da ba su ba ma’aikatar wa’adi bayan ta ba da hakuri, yanzu hakurinsu ya ƙare saboda shiru da gwamnatin ta ci gaba da yi.
Sanarwar ta ce:
“Ni da Barrista Abba Hikima mun yanke shawarar komawa kotu kan kuɗin N-Power da Ministan Harkokin Jinƙai, Nentawe, ya ce za a biya tun watan Yuli.
"Za mu koma kotu ƙarshen wannan wata bayan kotuna sun dawo daga hutun su domin ci gaba da shari’ar.
“Mun ba su wa’adi bayan sun ba da hakuri, amma yanzu hakurinmu ya ƙare domin ba mu ji daga wurinsu ba."
Yadda tsarin shirin N-Power yake a mulkin Buhari
Sun yi alƙawarin ci gaba da shari’ar har sai an biya duk kuɗaɗen da ake bin su, tare da jaddada cewa ba za a tauye haƙƙin matasan N-Power ba.
Matasa a Najeriya dai sun fara cin gajiyar shirin N-Power tun a lokacin mulkin marigayi Muhammasu Buhari a shekarar 2022.
Daga bisani, gwamnatin ta sake daukar wasu matasan a matsayin kashi na biyu domin rage matsin tattalin arziki a kasar.
Gwamnatin Tinubu za ta biya kudin N-Power
Kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana shirinta na biyan haƙƙokin ƴan N-Power da aka riƙe masu tun 2022.
Mataimakin shugaban Majajalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da hakan bayan wani taron sasanci da ya jagoranta a Abuja.
Ministan harkokin jin kai ya ce sun tarar da an sa kuɗin da za a biya ƴan N-Power a kasafin 2022 da na 2023 amma kuma ba a fitar da kuɗin ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

