An Cafke Dan Jarida bayan Fallasa Gazawar Gwamnatin Kebbi? An Samu Bayani
- Wasu bidiyoyi da aka yada kan halin da asibitoci su ke ciki a jihar Kebbi, sun jawo an taso gwamnati a gaba
- Gwamnatin Kebbi ta fito ta amince cewa daya daga cikin bidiyoyin na gaskiya ne amma akwai wanda tsohon bidiyo ne
- Hakazalika, gwamnatin ta yi magana kan zargin cewa ta sanya an garkame dan jaridar da ya wallafa bidiyoyin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi – Gwamnatin Kebbi ta yi magana kan bidiyon da ya nuna wasu marasa lafiya tsamo-tsamo cikin ruwa a wani asibiti.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kebbi, Yakubu Ahmed, ya bayyana cewa bidiyon da aka nuna marasa lafiya cikin asibitin da ambaliya ta mamaye a jihar tsohon bidiyo ne, ba na yanzu ba ne.

Source: Facebook
Yakubu Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Arise tv, ranar Asabar, 13 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kebbi ta yarda da bidiyo
Sai dai, kwamishinan ya tabbatar da cewa bidiyon da ke nuna wani mara lafiya a Asibitin Kangiwa kwance kan karfen gado babu katifa gaskiya ne.
Bidiyon, wanda dan jarida Hassan Mai-Waya Kangiwa ya wallafa, ya haifar da ce-ce-ku-ce da kuma damuwa kan yadda cibiyoyin kiwon lafiya ke tafiya a jihar.
Bayan wallafar bidiyon, rahotanni sun bayyana cewa an kama dan jaridar, lamarin da ya jawo karin ce-ce-ku-ce.
Me gwamnati ta ce kan cafke dan jarida?
Lokacin da aka tambaye shi kan inda dan jaridar yake, kwamishinan yada labaran ya bayyana cewa ya yi amanna cewa yana gida cikin iyalansa.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kebbi ko Gwamna Nasir Idris ba su bada wani umarnin a cafke kowa ba.
"Ina son yin amanna kan cewa dan jaridar yana gida. Ina son na aminta da hakan."
"Da farko dai, rahotannin da ke yawo cewa an cafke wani dan jarida saboda daukar hotuna, ba gaskiya ba ne."
"A wurin gwamnatin jihar Kebbi, babu wanda yake a tsare a bisa umarnin gwamnati ko gwamnan Kebbi."
- Yakubu Ahmed
A baya, Gwamna Nasir Idris ya dakatar da kwamishinan lafiya na jihar, Yunusa Musa-Ismail, bisa zargin sakaci wajen gudanar da ayyukansa.

Source: Facebook
Karanta wasu labaran kan jihar Kebbi
- PDP ta samu koma baya, tsohon sanatan Kebbi ya fice daga jam'iyyar
- Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da gonaki a Kebbi, gwamnati ta ba da tallafi
- Gwamnati ta fito da 'barnar' Malami a Kebbi, ta faɗi yadda tawagarsa ta riƙa harbin iska
Gwamnan jihar Kebbi ya nada sabon sarki
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi ya nada sabon sarki a masarautar Zuru, biyo bayan rasuwar mai martaba Muhammad Sani Sami Gomo II.
Dr. Nasir Idris ya amince da nadin Sanusi Mikailu a matsayin sabon sarkin masarautar Zuru inda zai maye gurbin marigayin.
Gwamnan na Kebbi ya amince da nadin ne bayan masu zaben sarki sun gabatar masa da sunan Sanusi Mikailu biyo bayan tantance mutanen da su ka nemi hawa kan kujerar sarautar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

