Mutuwa Mai Yankar Kauna: Matashin Dan Siyasa, Yunusa Yusuf Ya Rasu a Abuja

Mutuwa Mai Yankar Kauna: Matashin Dan Siyasa, Yunusa Yusuf Ya Rasu a Abuja

  • Hadimin shugaban karamar hukumar kwaryar birnin Abuja (AMAC), Yunusa Ahmadu Yusuf ya riga mu gidan gaskiya
  • Shugaban AMAC, Christopher Zakka Maikalangu ya yi ta'aziyya ga iyalai, abokai da sauran yan uwan mamacin
  • Ya bayyana Yunusa a matsayin matashi mai kwazo, wanda ya ba da gudummuwa mai tarin yawa wajen kawo ci gaba a Abuja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Mai taimaka wa shugaban karamar hukumar birnin Abuja (AMAC) na musamman kan harkokin ci gaban al'umma, Yunusa Ahmadu Yusuf ya rasu.

Shugaban AMAC, Hon. Christopher Zakka Maikalangu, ya yi alhini da jimamin rasuwar Yunusa, wanda ya bayyana da matashi mai kwazo da son ci gaban al'umma.

Yunusa Ahmadu Yusuf
Hoton matashin dan siyasa kuma hadimin shugagan karamar hukumar AMAC, Yunusa Ahmadu Yusuf Hoto: @realgazakure
Source: Twitter

Yunusa Yusuf ya rasu a ranar Juma’a bayan gajeriyar rashin lafiya, lamarin da ya girgiza al’umma da siyasar babban birnin tarayya (FCT), Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Lokaci ya kare: Babban basarake ya riga mu gidan gaskiya a Arewa ana cikin taro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da kakakin ciyaman din, Kingsley Madaki ya fitar yau Asabar, Maikalangu ya mika sakon ta'aziyya ga yan uwa da abokan arzikin mamacin.

Shugaban ya bayyana marigayin a matsayin ginshikin haɗin kai kuma jajirtaccen matashi mai yiwa jama’a hidima, wanda za a dade ba a manta da gudummawarsa ga ci gaban al’umma ba.

Shugaban AMAC ya yi ta'aziyyar Yunusa

Maikalangu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Yunusa, abokai, abokan aiki, da al’ummar Abuja baki ɗaya bisa wannan babban rashi.

Ya ce Yunusa mutum ne mai himma, jajirtaccen matashi, kuma mai kokarin haɗa gwamnati da al’umma a karamar hukumar AMAC da Abuja gaba ɗaya.

"Mafi yawan lokuta rayuwa ba ta da tsawo; wannan shi ne lokacin da muke buƙatarsa fiye da kowane lokaci, amma Allah ya fi mu sanin daidai.
"Za mu yi kewarka har abada, domin ka kasance jarumi, mai faɗin gaskiya, kuma ginshiki da nasarar da na samu a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin Ministan Tinubu da gwamna a APC? An samu bayanai

"Wannan rayuwa kankanuwa ce. Ka huta lafiya, sai mun sake haɗuwa ɗan uwa kuma aboki na,” in ji shi.

Hon. Maikalangu ya yi wa marigayin addu'a

Shugaban AMAC ya kuma roƙi iyalan marigayin, abokansa da al’ummar Abuja gaba ɗaya da su dauki rasuwarsa a matsayin ƙaddara daga Allah.

Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan Yunusa, ya kuma bai wa masu jimami musamman yan uwansa natsuwa da kwanciyar hankali, in ji rahoton Independent.

Birnin tarayya Abuja.
Hoton kofar shiga Babban Birnin Tarayya Abuja Hoto: @deeoneayekoto
Source: Getty Images

Sanarwar ta kuma yabawa jajircewar Yunusa wajen kare haƙƙin yan asalin Abuja, inda aka bayyana shi a matsayin babban mai fafutukar ’yancin 'yan asalin birnin tarayya.

Sanarwar ta kuma yabawa jajircewar Yunusa wajen kare haƙƙin yan asalin Abuja, inda aka bayyana shi a matsayin babban mai fafutukar ’yanc mazauna birnin tarayya.

Dalibar Kwalejin Fasaha ta rasu a Bauchi

A wani labarin, kun ji cewa wata dalibar difloma a Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, Barira Adam ta riga mu gidan gaskiya a dakin kwanan dalibai.

Barira, wacce ya rage kasa da wata guda ta fara jarabawar karshe, ta rasu ne yayin da take murmurewa daga wata doguwar rashin lafiya da ta yi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai yi jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya

Abokan karatunta sun bayyana ta a matsayin daliba mai jajircewa wadda ta dukufa wajen cimma nasarar a harkar neman ilimi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262