Taraba: An Tsinci Gawar Wanda Ake Zargi da Kisan Budurwarsa cikin Wani Irin Yanayi

Taraba: An Tsinci Gawar Wanda Ake Zargi da Kisan Budurwarsa cikin Wani Irin Yanayi

  • Bincike kan rasuwar daliba a jihar Taraba da ta rasu a dakin saurayinta ya dauki sabon salo bayan samun wasu bayanai
  • An tabbatar da cewa dalibar da ke tsangayar koyon aikin jarida, Comfort Jimtop ta rasu ne a dakin saurayinta wanda aka fara bincike
  • Kakakin rundunar yan sanda a Taraba, James Lashen ya tabbatarwa wakilin Legit Hausa cewa suna ci gaba da bincike

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Rundunar yan sanda na ci gaba da bincike bayan samun gawar wata dalibar jami'a a jihar Taraba.

Binciken game da rasuwar dalibar tsangayar koyon aikin jarida, Comfort Jimtop a jami’ar Taraba, ya dauki sabon salo bayan gano wasu bayanai.

An samu gawar saurayi da budurwarsa ta mutu a dakinsa
Saurayin marigayiya Comfort kenan, Emmanuel Kefas da aka tsinci gawarsa. Hoto: Adi Polycarp Yamusa.
Source: Facebook

Abin da 'yan sanda suka ce kan lamarin

Kakakin rundunar yan sanda a Taraba, James Lashen ya tabbatarwa wakilin Legit Hausa cewa suna ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

An bankado abubuwa, matar shedanin 'dan bindiga ta shiga hannu a Zamfara, ta tsure

Lashen ya ce suna jiran binciken da suka tura zuwa asibiti duk da cewa an samu wata kwalba dauke da wani sinadari mai hatsari.

Ya ce:

Muna jiran binciken da muka tura asibiti domin tabbatar da lamarin, mun samu wata kwalba ta roba dauke da wani sinadari da ake zargin akwai giya a ciki."

Rahoton The Guardian ya ce lamarin ya sauya ne bayan gano gawar Emmanuel Kefas, babban wanda ake zargi.

An gano gawar Kefas a ranar Juma’a a Tudiri a karamar hukumar Ardo-Kola, cikin yanayi mai rikitarwa da kara tayar da hankula a jihar Taraba.

Har ila yau, James Lashen, ya tabbatar da cewa shugaban kauyen Tudiri ne ya kai rahoton gano gawar a ofishinsu.

Yan sanda suka ce:

“An gano gawarsa a Tudiri, kuma an samu waya hannu kirar Tecno Android a gefenta.
“Lokacin da aka caje wayar, masu bincike sun gano hoto da marigayin tare da Comfort Jimtop, abin da ke nuna suna cikin soyayya."

Kara karanta wannan

Mutum 4 sun mutu, wasu sun raunata da yan bindiga suka farmaki wajen jana'iza

Yan sanda suna binciken mutuwar budurwa da saurayi a Taraba
Tawirar jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas. Hoto: Legit.
Source: Original

Matakin da 'yan sanda suka dauka

Lashen ya kara da cewa an kai gawar asibitin FMC Jalingo domin bincike, tare da kokarin tabbatar da asalin wanda ya mutu daga danginsa.

‘Yan sanda sun ce ba a tabbatar da musabbabin mutuwar Kefas ba tukuna, ko kashe kai ne, ko kisa, ko hatsari, bincike na ci gaba.

Rasuwar Comfort ta tayar da hankula a jihar tun farko, dalibai da kungiyoyi na bukatar a samu adalci, inda Kefas ya zama wanda ake zargi.

Wannan sabon bayanai game da binciken ya jefa tambayoyi da shakku kan lamarin wanda ke kara rura wuta a cikin al’umma.

An tsinci gawar budurwa a dakin saurayi

Mun ba ku labarin cewa an tsinci gawar wata dalibar aji uku a jami'ar Port Harcourt, Otuene Justina Nkang, a dakin saurayinta.

Wanda ake zargin da ke zaune a wani babban yanki na Port-Harcourt ya kashe Nkang sannan ya yanyanka sassan jikinta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki harama, nan ba da jimawa ba za a daina dauke wuta a Najeriya

Yan banga ne suka cafke wanda ake zargin a lokacin da yake kokarin jefa gawar da ta rube a wani bola wanda lamarin ya tayar da hankulan al'umma a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.