Ministar Tinubu Ta Dauki Mataki bayan Ma'aikata Sun Gudanar da Zanga Zanga a Kanta

Ministar Tinubu Ta Dauki Mataki bayan Ma'aikata Sun Gudanar da Zanga Zanga a Kanta

  • Ministar harkokin mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta yi magana kan zanga-zangar da ma'aikata su ka yi a kanta
  • Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim ta bukaci hadin kai da tattaunawa a matsayin hanya mafi kyau wajen shawo kan matsaloli
  • Hakazalika, ministar ta raba kayan tallafi ga ma'aikatan da su ka gudanar da taro don samo mafita ga korafe-korafen da ake yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministar harkokin mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta yi magana kan zanga-zangar da ma'aikata su ka yi kan korafe-korafen da su ke da su a kanta.

Ministar ta bayyana cewa ta yafewa ma’aikatan da su ka yi zanga-zanga kan walwalarsu da yanayin aiki, tare da yin alkawarin kara mayar da hankali wajen kula da jin dadin ma’aikata.

Ministar harkokin mata ta yafewa ma'aikata
Hoton ministar harkokin mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, tana jawabi Hoto: @hm_womenaffairs
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Jonathan Eze, ya fitar.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya samu gargadi bayan ma'aikatan jinya sun shiga yajin aiki a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana hakan ne a yayin taron tattaunawa tsakanin shugabancin ma’aikatar da ma’aikata a Abuja ranar Juma’a, 12 ga watan Satumban 2025.

Me ministar mata ta ce kan zanga-zangar?

Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim ta jaddada muhimmancin hadin kai, girmamawa da tattaunawa wajen shawo kan matsalolin cikin gida, rahoton The Guardian ya tabbatar da labarin.

Hakazalika, ministar ta ce ba ta rike wani ma'aikaci a zuciya ba kan zanga-zangar.

“Ya kamata mu kasance mutane kafin komai. Hadin kai shi ne kadai hanyar cigaba. Ban dauki wani abu a raina kan kowa ba, kuma na yi imani za mu iya magance matsalolinmu ta hanyar tattaunawa da girmama juna."

- Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim

Ta bayyana ma’aikatar harkokin mata a matsayin wuri mai muhimmanci, wanda ke da alhakin kare hakkin mata, yara, iyalai da sauran masu rauni a cikin al’umma.

Minista ta yi alkawarin kulawa da ma’aikata

Ministar ta tabbatar da cewa kula da walwalar ma’aikata na daga cikin abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, duk da cewa wasu daga cikin alhakin gudanarwa na hannun babban sakatare da daraktoci.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Gwamnati ta bankado ma'aikatan bogi a Bauchi, za su fuskanci hukunci

A matsayin alamar kyautatawa, ministar ta sanar da ba da kyautar buhun shinkafa mai nauyi kilo 50 ga kowane ma’aikacin da ya halarci taron.

Ma’aikata sun yarda yin zanga-zanga kuskure ne

Shugabar kungiyar ma’aikata, Mrs. Anne Orjiobele, tare da Kwamared Success Alake da sauran wakilai, sun amince cewa an yi zanga-zangar ne bisa kuskure, inda suka yi alkawarin goyon bayan ministar.

Ministar mata ta yafewa ma'aikata kan zanga-zanga
Hoton ministar harkokin mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim Hoto: @hm_womenaffairs
Source: Twitter

Sun kuma sake rokon a ci gaba da kula da walwalarsu, tare da bayyana cewa rashin fahimtar da ya jawo rikicin bai da wani nufi na jayayya kai tsaye.

A yayin taron, ma’aikatan sun kara gabatar da bukatu kan batun gidaje da damar samun horaswa.

Ministar ta tabbatar musu cewa za a yi iya kokari a warware wadannan matsaloli bisa ga iya abin da za ta iya yi.

Shugaba Bola Tinubu ya yabawa Sarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kwararo yabo ga wani Sarki a Arewacin Najeriya.

Shugaba Tinubu ya yabawa Sarkin kasar Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, bisa ga kokarin da ake yi wajen hada kan al'umma.

Kara karanta wannan

Ma'aikata sun yi zanga zanga, an yi zarge zarge kan ministar Tinubu

Mai girma Bola Tinubu ya yi yabon ne yayin da yake taya basaraken murnar cika shekara 73 a duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng