An kai Dan Ta'addan Najeriya da Ya kai Hari Ofishin Majalisar Dinkin Duniya Kotu

An kai Dan Ta'addan Najeriya da Ya kai Hari Ofishin Majalisar Dinkin Duniya Kotu

  • Kotu ta ba da umarni a hanzarta shari’ar Khalid Al-Barnawi da wasu huɗu da ake zargi da harin ginin UN a Abuja a 2011
  • Mai shari’an ya amince a kunna bidiyon da DSS ta gabatar domin tabbatar da amincewar furucin wadanda ake zargi
  • Biyo bayan hukuncin, shari’ar za ta ci gaba a ranar 23 da 24 ga Oktoba, 2025 bayan jinkiri da dama da ta fuskanta tun 2016

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCt, Abuja – Babbar kotun tarayya ta amince da buƙatar hukumar DSS domin hanzarta shari’ar Khalid Al-Barnawi da ake zargi da kitsa hari a ofishin majalisar dinkin duniya a 2011.

Al-Barnawi da ake zargi da zama babban kwamandan ƙungiyar Ansaru na fuskantar tuhuma tare da wasu mutum huɗu a kan laifuffukan ta’addanci.

Kara karanta wannan

NNPCL: Mele Kyari ya yi magana bayan EFCC ta masa tambayoyi kan almundahana

Kofar shiga kotun tarayya da ke Abuja
Kofar shiga kotun tarayya da ke Abuja. Getty Images
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa shari'ar da ta sha jinkiri tun daga kama shi a 2016, ta shiga sabon mataki bayan kotu ta ɗauki matakan tabbatar da gaggauta bincike da sauraron shaidu.

Hukuncin kotu kan bukatar DSS

A zaman kotun da aka yi a ranar Juma’a, lauyan DSS, Alex Iziyon, ya gabatar da bukatar a hanzarta shari’ar, yana mai cewa hukumar ta shirya tsaf don tabbatar da kammala ta cikin lokaci.

Lauyan wadanda ake tuhuma bai yi adawa da wannan bukata ba, abin da ya sa mai shari’a Emeka Nwite ya amince da ita.

Kotun ta bayar da umarnin a kunna bidiyon da DSS ta gabatar a gabanta domin bangarorin biyu su dauki bayanai kafin komawa kotu a rana ta gaba.

Dalilin kunna bidiyo a kotun Najeriya

Mai shari’a Nwite ya bayyana cewa kunna bidiyon na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa furucin da wadanda ake tuhuma suka yi sun fito daga gare su ne ba tare da tilastawa ba.

Kara karanta wannan

Ana kukan farashin taki, Shettima ya ce a raba wa manoma Naira biliyan 250

Ya kara da cewa wannan tsari zai bada damar kaucewa jinkirin da zai iya sake kawo tsaiko a cigaban shari’ar.

Bayan haka, kotu ta dage zaman zuwa ranar 23 da 24 ga watan Oktoba domin ci gaba da sauraron kara.

Hafsun tsaron Najeriya, Janar Musa
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Musa. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Tarihin kama Al-Barnawi da shari’arsa

An kama Khalid Al-Barnawi a Lokoja, jihar Kogi, a watan Afrilu na 2016, shekaru biyar bayan harin da ya hallaka fiye da mutane 20 tare da jikkata wasu sama da 70 a Abuja.

Daily Post ta rahoto cewa tun daga lokacin, shari’ar ta fuskanci tsaiko saboda matsalolin doka da na gudanarwa, abin da ya sa ake ta jinkiri wajen yin hukunci.

Masu tuhuma sun bayyana cewa tsakanin 2011 zuwa 2013, Al-Barnawi da abokan harkallarsa sun yi shirya kai hare-haren ta’addanci a jihohin Arewa kamar Sokoto, Kebbi, Bauchi, Borno da Gombe.

Maganar kasar Amurka kan Al-Barnawi

Sauran wadanda ake tuhuma tare da Al-Barnawi sun hada da Mohammed Bashir Saleh, Umar Mohammed Bello (Datti), Mohammed Salisu da Yakubu Nuhu (Bello Maishayi).

Al-Barnawi ko tun a 2012 Amurka ta ayyana shi a matsayin dan ta'addan duniya tare da sa kyautar Dala miliyan 5 (sama da N7bn) ga duk wanda ya ba da bayanin da zai kai ga cafke shi.

Kara karanta wannan

A karshe, Kotun Abuja ta yanke hukunci kan shugaban Ansaru da aka cafke

An kama 'yan ta'adda a Zamafara

A wani rahoton, kun ji cewa an kama wasu 'yan bindiga da suka kai hari wani masallaci a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama mutum shida daga cikin maharan da suka nufi afkawa Musulmi a masallaci.

Bincike ya nuna cewa 'yan ta'addan sun kai farmaki ne a yankin Dansadau da ke jihar Zamfara ana sallar Asuba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng