Lokaci Ya Yi: Dalibar Kwalejin Fasaha a Najeriya Ta Rasu a Dakin Kwanan Dalibai
- An shiga jimami da alhini da Allah ya karbi ran wata dalibar difloma a Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, Barira Adam
- Hukumar makarantar ta tabbatar da lamarin, ta ce Barira ta rasu da yammacin ranar Alhamis bayan fama da rashin lafiya
- Rahotanni sun nuna cewa ta yi rubutu mai alaka da shirin kammala karatunta a shafin sada zumunta da safiyar ranar da za ta rasu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke jihar Bauchi ta shiga jimami da alhini bisa rasuwar daya daga cikin dalibanta mata da ke shirin kammala karatu.
Dalibar da ke aji na biyu a difloma (ND II) a sashen koyon aikin jarida watau 'Mass Communication', Barira Adam, ta rasu a daren ranar Alhamis.

Source: Facebook
Hukumar kwalejin ta tabbatar da rasuwar Barira a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook da safiyar jiya Juma'a, 12 ga watan Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya yi sanadin rasuwar Barira Adam?
Dalibar dai ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya a cikin gidan kwana na dalibai mata da ke harabar makarantar.
Barira, wacce ya rage kasa da wata guda ta fara jarabawar karshe, ta rasu ne yayin da take murmurewa daga wata doguwar rashin lafiya da ta yi.
An ce a safiyar ranar da za ta rasu, ta sanya hotonta a manhajar WhatsApps, tare da rubutun cewa, “kwanaki masu kyau suna zuwa nan ba da daɗewa ba."
Abokan karatunta sun bayyana ta a matsayin daliba mai jajircewa wadda ta dukufa wajen cimma nasarar a harkar neman ilimi, in ji rahoton Leadership.
Hukumar makarantar ta yi alhinin rasuwar Barira tare da mika sakon ta'aziyya ga danginta da abokan karatu da al'ummar kwalejin gaba daya.
Hukumar Kwalejin Fasahar ta yi ta'aziyya
Shugaban makarantar, Alhaji Sani Usman, ya yi ta'aziyyya cikin alhini ga iyalinta, abokan karatu, sashen da take karatu da kuma ƙawayenta.
Sanarwar hukumar kwalejin ta ce:
"Da zuciya mai nauyi tare da mika wuya ga ikon Allah (SWT), hukumar Kwaleji na sanar da rasuwar daliba ta shekara ta biyu (ND II) a sashen Mass Communication, Barira Adam.
"Ta rasu ne da yammacin ranar Alhamis 11 ga Satumba, 2025 bayan gajeriyar rashin lafiya. Allah Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya kuma ba ta Aljannatul Firdaus.
"Shugaban makaranta, Alhaji Sani Usman, a madadin daukacin al’ummar Kwalejin, ya mika ta’aziyya ga iyalinta na kusa, abokan karatu, sashen koyon aikin jarida da kuma ƙawayenta.
"Allah Ya ba mu duka hakurin jure wannan babban rashi."

Source: Facebook
Bako daga Masar ya rasu a otal a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa an shiga tashin hankali a wani otal da ke Abuja yayin da bako daga kasar Masar, Mohammed Saleh ya fadi ya mutu kwatsam.
Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya gamu da ajali ne a lokacin da yake cin abincin dare tare da wasu mutane a otal din a ranar Juma'a.
An tattaro cewa shugaban jami'an tsaron otal ɗin, Francis Yusuf, ne ya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda na Wuse da ke cikin Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


