Lokaci Ya Kare: Babban Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Arewa Ana cikin Taro

Lokaci Ya Kare: Babban Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Arewa Ana cikin Taro

  • Jihar Kogi ta shiga jimami bayan rasuwar Mai Martaba, Alhaji Aminu Kawu Akuh, Sarkin Elaite, wanda ya taka rawar gani a masarautar
  • Tsohon ɗan takarar gwamnan SDP, Yakubu Muritala Ajaka, ya bayyana cewa marigayin mutum ne mai son zaman lafiya da tsaya mutanensa
  • Ajaka ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayin da al’ummar Elaite, yana addu’ar Allah ya gafarta masa ya karɓe shi cikin Aljannah Firdaus

'Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Jihar Kogi ta yi babban rashi da aka sanar da rasuwar fitaccen basarake wanda ya bayar da gudunmawa a jihar.

An tabbatar da rasuwar marigayin Sarkin Elaite da ke karamar hukumar Ajaokuta a jihar da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Ajaka ya jajanta da Sarki ya rasu a Kogi
Sarkin Elaite a Kogi da Yakubu Murtala Ajaka. Hoto: @MuritalaAjaka.
Source: Twitter

An yi rashin babban Sarki a Kogi

Hakan na cikin wata sanarwa da tsohon dan takarar gwamnan jihar a SDP, Muritala Ajaka ya tabbatar da sanarwa a shafin X.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware Sarki 1 a Arewa, ya kwarara masa yabo kan abubuwan alheri da yake yi

'Dan siyasar ya bayyana jimaminsa na rasuwar Mai Martaba, Alhaji Aminu Kawu Akuh wanda ya rasu a makon jiya.

Ajaka ya bayyana cewa marigayin mutum ne mai son zaman lafiya wanda ya sadaukar da ransa ga al'umma.

Ajaka ya yi rubutu kamar haka:

"Ina alhinin rasuwar Mai Martaba Alhaji Aminu Kawu Akuh, Sarkin Elaite a Karamar Hukumar Ajaokuta.
"Mutum ne mai son zaman lafiya, hikima da sadaukar da kai, wanda rayuwarsa ta kasance don jin daɗin jama’arsa.
"Rasuwarsa babban rashi ne ga masarautar gargajiya, ga Jihar Kogi, da ma Najeriya baki ɗaya."
Sarkin Elaite a jihar Kogi ya rasu
Marigayi Sarkin Elaite a Kogi, Alhaji Aminu Kawu Akuh. @MuritalaAjaka.
Source: Twitter

Murtala Ajaka ya yi jimamin mutuwar Sarki

Muritala Ajaka ya mika sakon ta'aziyya ta musamman ga iyalana marigayin da kuma al'ummar Elaite da dukan jama'ar Ajaokuta.

Ya yi addu'ar Ubangiji ya yi masa rahama ya sanya shi gidan aljanna firdausi madaukakiya.

Ya kara da cewa:

"Ina mika ta’aziyyata ga iyalinsa, al’ummar Elaite, da dukkan jama’ar Ajaokuta, Allah Madaukaki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma karɓe shi cikin Aljannah Firdaus. Ameen."

Kara karanta wannan

Mutuwa ta taba sarakuna, Wamban Dawakin Zazzau ya rasu a gadon asibiti

An tattaro cewa Sarkin ya rasu ne a ranar Laraba 10 ga watan Satumbar 2025 yayin taro mai muhimmanci a Okene, inda aka ga alamun rashin lafiya a jikinsa.

“Ya fadi a taron jim kaɗan bayan yin addu’a, an garzaya da shi asibiti amma di aka tabbatar da cewa ya rasu."

- In ji majiya ta kusa da shi

Rahotanni sun tabbatar da cewa an riga an birne marigayin bisa ga tsarin addinin Musulunci a safiyar ranar Alhamis 11 ga watan Satumbar 2025.

An yi rashin wani Sarki a Najeriya

Mun ba ku labarin cewa an kara yin babban rashi a Najeriya da Sarkin Arigbajo, Mai Martaba Timothy Oluwole Sunday Mosaku ya rasu yana da shekara 89.

Iyalansa sun tabbatar da rasuwar basaraken a wata sanarwa da suka rabawa manema labarai a yau Juma'a, 22 ga watan Agusta, 2025.

Sanarwar ta bayyana tsare-tsaren jana'izar Marigayi Sarkin wanda za a yi a ranaku biyu a watan Satumba mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.