An Turo Sako daga Kasashen Waje, Ana So Gwamna Ya Soke Nadin Sarki a Najeriya

An Turo Sako daga Kasashen Waje, Ana So Gwamna Ya Soke Nadin Sarki a Najeriya

  • Nadin Sarkin Isara-Remo da ke jihar Ogun ya zo da tangarda bayan masu alhakin zabe sun zabi Bashorun Oluwole Ogunbayo
  • 'Yan asalin Isara-Remo da ke zaune a kasahen waje da wasu da ke nan gida sun yi fatali da wannan, sun ce ba a bi doka da tsarin al'ada ba
  • Sun shigar da korafi gaban Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, sun roki ya yi amfani da damarsa wajen gyara kuskuren da aka yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - ’Yan asalin Isara-Remo da ke ƙaramar hukumar Remo ta Arewa a jihar Ogun, sun koka kan tsarin da aka bi wajen zaɓen sabon Odemo na Isara-Remo, Bashorun Oluwole Ogunbayo.

Jama'ar yankin masarautar sun yi zargin cewa masu alhakin zaben Sarki ba su bi hanyar da doka da al'adar gargajiya ta shimfida ba wajen zabo mai martaba.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin Ministan Tinubu da gwamna a APC? An samu bayanai

Jihar Ogun.
Hoton taswirar jihar Ogun a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Vanguard ta ce mutanen, ƙarƙashin inuwar kungiyar Concerned Youths of Isara-Remo, daga gida da ƙasashen waje, sun tura korafi ga Gwamna Dapo Abiodun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bukaci gwamnan Ogun ya soke nadin Sarki

Sun roki gwamnan ya yi amfani da ikon da kubdin tsarin mulki ya ba shi, ya soke tsarin da aka biyo aka zabi Ogunbayo a matsayin sabon Sarkin Isara-Remo.

Sannan sun bukaci Gwamna Abiodun ya umurci masu zaben sarauta da su bi ƙa’idodi da kuma al’adar gargajiya wajen zaɓen sabon Sarki.

Shugaban kungiyar yan asalin Isara-Remo, Wale Odetola da sakatarensa, Kola Okusanya sun rattaba hannu a takardar korafe-korafen da suka mika wa gwamnan Ogun.

Abubuwan da ake zargi a zaben Sarkin Remo

Sun zargi cewa tsarin da aka bi wajen nada Ogunbayo a matsayin Sarki cike yake da kura-kurai kamar cin hanci, barazana, tilastawa, da kuma amfani da sunan masu nadi ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan bindigan da suka kai hari masallaci ana sallar asuba

A cikin ƙorafi na farko da aka rubuta ranar 11 ga Satumba, 2025, ’yan asalin yankin da ke ƙasashen waje tare da matasan garin sun roƙi gwamna da ya kafa kwamitin bincike.

Haka kuma sun koka kan yadda aka yi amfani da dakarun tsaro wajen tsoratar da al’umma a lokacin zaɓen ranar 8 ga Satumba, 2025, in ji rahoton Punch.

Gwamna Dapo Abiodun.
Hoton gwamnann jihar Ogun Dapo Abiodun Hoto: Prince Dapo Abiodun
Source: Twitter
“Mu a matsayinmu na masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da zaman lafiya, ba za mu iya yin shiru ba yayin da ake lalata tsarin al'adunmu da barazana da cin hanci," in ji su.

Odetola da Okusanya sun ƙara da cewa kujerar Sarkin Isara-Remo wata alama ce ta haɗin kai da amana tsakanin ’ya’yan garin.

Shirin tsige Sarki ya fara tayar da rigima

A wani labarin, kun ji cewa rikici ya barke tsakanin 'ya'yan gidan sarauta na masarautar Ipetumodu a wurin wani taron da suka gudanar a jihar Osun.

Wannan rigima da aka yi dai na zuwa ne bayan kira ga Gwamnan Osun ya tsige Sarkin Ipetumodu saboda hukuncin da kotun Amurka ta yanke masa.

Kotun Amurka ta yanke wa basaraken hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni 56, lamarin da ya jawo aka fara tunanin tsige shi daga mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262