Bayan Buhari Ya Rufe Iyakoki, Tinubu Ya Bude Su domin Karya Farashin Abinci
- Ministan noma Abubakar Kyari ya bayyana cewa matakan gaggawa na Bola Tinubu kan abinci sun rage tsadarsa
- Ya bayyana cewa an bude kofar shigo da abinci Najeriya na ɗan lokaci don daidaita gibin da ake da shi a cikin gida
- Kyari ya tabbatar da cewa matakan sun fara haifar da sauyi a kasuwa kuma ana ƙara samar da taki da kayan tallafi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, ya ce matakan gaggawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka tun a 2023 kan abinci sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Sanata Kyari ya tabbatar da cewa farashin abinci ya ragu sosai a kasuwannin Najeriya saboda matakin da aka dauka.

Source: Facebook
Ministan ya bayyana haka ne a tattaunawa da aka yi da shi a tashar Arise News a safiyar Juma’a, inda ya kare dabarun gwamnatin Tinubu a kan noma da samar da abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, an ɗauki matakan ne domin magance manyan matsalolin fannin noma, waɗanda suka janyo karancin abinci da tsadar kayan masarufi a Najeriya.
Dalilin ɗaukar matakan gaggawa
Sanata Kyari ya ce Shugaba Tinubu ya karɓi mulki a wani lokaci mai matuƙar wuya, inda matsalolin abinci suka yi tsanani.
Leadership ta wallafa cewa ya ce wannan ne ya sa ya ayyana dokar ta baci kan sha'anin abinci a watan Yulin 2023.
Ya bayyana cewa matsalar tana da alaƙa da rashin daidaito a tsakanin samar da abinci da yadda ake bukatarsa a Najeriya.

Source: Twitter
Alal misali, ministan ya ce akwai gibin kusan kashi 15 a fannin shinkafa tsakanin abin da ake samarwa a gida da kuma abin da ake buƙata.
Don haka, ya ce gwamnati ta haɗa shirin ƙarfafa manoma da kuma shigo da kayan abinci na ɗan lokaci don cike gibi.
Bola Tinubu ya bude iyakoki na wata 6
Ministan ya bayyana cewa shirin shigo da abinci ta iyakoki bai wuce na wata shida ba, kuma an kammala shi a yanzu.
Ya ce ba a yi hakan don rage ƙwazon manoma ba, illa kawai don daidaita kasuwa ne a lokacin da ake cikin tsananin buƙata.
Ya ƙara da cewa shigo da abinci bai kai yadda zai hana manoma ci gaba da noma ba, domin gwamnati ta haɗa shi da shirye-shiryen tallafa musu.
A lokacin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ne aka rufe iyakokin Najeriya domin habaka noma a cikin gida.
Tallafin Tinubu ga manoman Najeriya
Daga cikin matakan da Tinubu ya dauka, Kyari ya ce ya ba da umarnin a saki buhunan taki miliyan biyu don rabawa manoma kyauta ba tare da an biya ko sisin kwabo ba.
Bugu da ƙari, ministan ya ce an rage kuɗin taki zuwa rabi domin ƙara wa manoman Najeriya ƙarfin gwiwa.
Wannan ya sa, a cewarsa, an samu ƙarin amfanin gona a shekarar 2024 fiye da yadda ake tsammani.
Farashin abinci ya ragu inji Kyari
A ƙarshe, Ministan ya tabbatar da cewa duk waɗannan matakan sun fara nuna tasirinsu a kasuwa.
Ya ce yanzu farashin abinci ya sauka, lamarin da ya ba da kwarin gwiwa ga gwamnati da al’umma gaba ɗaya.
A shekarar 2023, Tinubu ya nada Sanatan na Borno ta Arewa a matsayin Minista, kafin nan ya rike matsayi a jam'iyyar APC.
Tinubu ya ce a karya farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a karya farashin abinci.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke cigaba da kokawa kan yadda kudin kayan masarufi ke lakume mafi yawan albashinsu.
Umarnin shugaban kasar kan rage farashi ya shafi rage kudin da ake kashewa wajen jigilar abinci a fadin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


