Murna Ta Koma Ciki? Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Shirin Daukar Sababbin Ma'aikata
- Hukumar FCT-CSC ta nesanta kanta daga tallan neman sababbin ma'aikata a babban birnin tarayya Abuja a baya-bayan nan
- Wani talla d ake yawo ya bayyana cewa akwai guraben aiki akalla 3,000 da hukumar kula da ma'aikatan Abuja za ta cike
- A sanarwar da ta fitar, hukumar ta ce wannan aikin yan damfara ne, kuma akwai sahihiyar hanya da jama'a za su gane hakan a gaba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya a Babban Birnin Tarayya (FCT-CSC) ta fitar da gargadi ga jama’a dangane labarin daukar sababbin ma'aikata.
Hukumar ta ce ana tallan bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke ikirarin cewa akwai guraben aiki 3,000 da ake bukatar a cike su.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: Gwamnati ta bankado ma'aikatan bogi a Bauchi, za su fuskanci hukunci

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa acewar hukumar, wannan talla wata dabara ce ta masu damfara da ke kokarin yaudarar matasa da masu neman aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Abuja ta karyata neman ma'aikata
Daily Post ta ruwaito hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya, ta cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ya kamata jama'a su hankalta.
Ya bayyana cewa:
"An janyo hankalin Hukumar FCT-CSC kan wani talla da ke yawo a dandalin sada zumunta da ke kiran masu neman aiki da su cike guraben aiki 3,000 da babu su."
"Muna so mu jaddada cewa wannan talla ƙarya ce. Aikin wasu masu damfara ne da ke kokarin cutar da jama'a, musamman matasan da ke neman aiki."
'Babu tsarin daukar ma'aikata,' Gwamnati
Hukumar ta bayyana cewa babu wani tsarin daukar ma’aikata da ta ke gudanarwa a halin yanzu, kuma ba ta da wata alaka da irin wannan talla da ke yawo.

Kara karanta wannan
Hukumar kwastam: Mutane kusan 600,000 sun nemi guraben aiki da ba su kai 4,000 ba
Ta roki jama’a da su yi watsi da wannan sanarwar da ba ta da tushe, sannan su rika ziyartar ofishin hukumar domin karin bayani
Hukumar ta bukaci duk wanda ke da shakku ko tambaya game da aikin hukumar da ya kai ziyara kai tsaye ofishinta na hedikwata da ke ginin APDC a birnin Abuja.

Source: Facebook
Tun bara ne gwamnatin tarayya ta amince da kafa hukumar domin bayar da damar ci gaba da aiki da kula da sauran al'amuran ma'aikata.
Wannan matakin ya bayar da dama ga ma’aikatan FCT su kai matsayin manyan sakatarori da kuma karin girma yadda ya kamata.
Daga karshe, hukumar ta sake nanata kira ga jama’a da su kasance masu lura da irin wadannan shafuka da ke yada labaran karya, tare da kauce wa fadawa tarkon mayaudara.
Gwamna ya kori ma'aikata
A wani labarin, mun wallafa cewa Gwamnatin jihar Abia ta kori ma’aikata shida saboda zargin sun karɓi albashi da ya zarce abin da ya dace ta hanyar jirkita tsarin albashin.
Gwamnan jihar, Alex Otti ya bayar da umarnin a ƙara zurfafa bincike don gano duk waɗanda ke da hannu, ciki har da waɗanda suke aikata hakan daga ofishin biyan albashi.

Kara karanta wannan
'Sun fara kamfe a sakaye,' INEC ta fadi yadda 'yan siyasa su ke birkita mata lissafin 2027
Sunayen waɗanda aka kora daga aiki sun haɗa da; Dickson Uche Eze, Esther Emeruwa, Ijeoma Jonathan, Treasure Isinguzo, Chioma Victoria Erondu da kuma Hannah Ezinne Eze.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng