Ana Kukan Farashin Taki, Shettima Ya Ce a Raba wa Manoma Naira Biliyan 250
- Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya umarci PFSCU ta hanzarta rabon lamunin Naira biliyan 250 ga kananan manoma
- Ya bukaci samar da ingantaccen hanyar aiwatar da shirin don tabbatar da cewa kuɗin ya isa ga manoma a Najeriya cikin lokaci
- Gwamnonin jihohi da dama sun yaba da shirin tare da roƙon a ƙara tallafi ga manoma domin tabbatar da wadatar abinci a kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya umarci hukumar PFSCU da ta hanzarta raba lamunin Naira biliyan 250 da aka ware don tallafawa kananan manoma.
Shettima ya bayyana wannan umarni ne a yayin taron kwamitin PFSCU karo na shida da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Source: UGC
A sakon da hadiminsa ya wallafa a X, ya ce wajibi ne a samar da ingantaccen tsari domin guje wa jinkiri da kuma tabbatar da cewa an kai tallafin ga manoman da aka nufa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da cikakken goyon baya wajen sauƙaƙe harkokin taki da samar da iri, lamarin da ya kara karfafa aikin PFSCU.
Za a raba wa manoma kudi a Najeriya
Shettima ya ce za a tattauna tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki domin samar da cikakkiyar hanya wacce za ta tabbatar da cewa kuɗin sun isa ga manoma da aka nufa.
Ya ce hakan zai samar da ƙarin amfanin gona mai yawa a Najeriya da bunkasa samar da abinci a ƙasar nan.
Ya yaba da nasarorin PFSCU da cewa haɗin gwiwar ma’aikatun gwamnati, masu zaman kansu da ƙungiyoyi na taimakawa wajen aiwatar da manufofin da aka tsara.
Martanin gwamnonin jihohi kan shirin
Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi kira da a gina tsarin da zai tabbatar da cewa rancen ya isa ga manoma kai tsaye, tare da bayar da tabbacin cewa jiharsa za ta tallafa wa PFSCU da kudi.
Haka nan Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba da aikin Bankin Noma, amma ya jaddada bukatar a samar da karin tallafin ga manoman cikin gida.
Shi kuwa Gwamnan Cross River, Sanata Bassey Otu, ya goyi bayan batun rance amma ya bukaci ƙara wa manoma kwarin gwiwa ta hanyar tallafin gwamnati.

Source: Facebook
Rawar PFSCU da nasarorin da ta samu
A cikin bayaninta, shugabar PFSCU, Marion Moon, ta bayyana cewa har yanzu mutane miliyan 30.8 a Najeriya na fama da ƙarancin abinci, don haka akwai bukatar inganta tsaron abinci.
Ta ce PFSCU ta samu ci gaba sosai wajen haɗin gwiwa da hukumomi a dukkan matakan gwamnati.
Vanguard ta wallafa cewa daga cikin nasarorin da aka samu tun watan Afrilu akwai samar da inshora ga manoma 250,000 a ƙarƙashin shirin NAPM da sauransu.
Za a dauki sunayen manoma a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya za ta fitar da shiri na musamman game da tallafawa manoma.
A karkashin shirin, an bayyana cewa za a dauki sunayen manoma na asali da sauran bayanan su domin tantance su.
An ce hakan ya zama wajibi ne domin kaucewa mika tallafin ga wadanda ba su cancanta ba ko kuma wadanda ba manoma ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


