Sabon Salo: Gwamna Ya Kakaba Doka kan Sanya Sutura a Jiharsa, an Tabo Masu Gemu

Sabon Salo: Gwamna Ya Kakaba Doka kan Sanya Sutura a Jiharsa, an Tabo Masu Gemu

  • Gwamnatin jihar Delta ta sabunta dokar suturar ma’aikata wanda ya jawo maganganu daga bangarori da dama
  • A dokar da ake shirin sabuntawa, zata hana tara gemu mai yawa da wasu kaya da ba su dace ba ga ma'aikatan jihar
  • Gwamnatin ta ce shugabanni da manyan jami’ai za su jagoranci aiwatar da dokar, tare da hukunta duk wanda ya karya ka’ida

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Gwamnatin jihar Delta za ta sabunta dokar sanya sutura ga ma’aikata da ke fadin jihar baki daya.

Gwamnatin jihar ta yi gargadi na musamman cewa ba za ta lamunci rashin dacewar sanya sutura ba a tsakanin ma'aikata.

Gwamna zai sabunta dokar sanya sutura a jiharsa
Gwamnan jihar Delta da ke Kudancin Najeriya, Sheriff Oborevwiri. Hoto: Rt Hon. Sheriff Oborevwori.
Source: Facebook

An sabunta dokar sanya sutura a jihar Delta

Takardar da ofishin shugaban ma’aikata ya sanya hannu ta bayyana cewa an sabunta dokar ne domin kare mutunci da kimar ma’aikata, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Gwamnati ta bankado ma'aikatan bogi a Bauchi, za su fuskanci hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce an samar da tsohuwar dokar ce a ranar 12 ga Maris, 2009 wanda yanzu aka sabunta ta domin hana amfani da sutura marasa kyau.

Gwamnatin jihar ta umurci manyan jami’ai su zama jakadu wajen nuna kyakkyawan sutura tare da gyara ƙasa da su ta hanyar hukunta masu karya doka.

Yanayin suturar ma'aikata maza a Delta

Ga maza, an ce duk jami’an da ke mataki na 13 zuwa sama su rika zuwa aiki da cikakkiyar riga da ake kira 'suit; 'ban da ma’aikatan da ke sanye da kaya na musamman.

Haka kuma ma'aikata da ke mataki na 07-12 za su iya sanya 'suit' ko wando, riga da madaurin wuya, yayin da mataki na 01-06 na su ke da sauƙi.

An ba da izinin sanya kaya na gargajiya ga maza kawai ranar Juma’a da lokuta na musamman, amma ba tare da tara gemu mai yawa ba.

Gwamnati ta sabunta dokar sanya kaya, ta yi gargadi kan gemu
Gwamna Sheriff Oborevwori kenan na jihar Delta a ofishinsa. Hoto: Rt. Hon. Sheriff Oborevwori.
Source: Facebook

Suturar da aka warewa mata a Delta

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam: Mutane kusan 600,000 sun nemi guraben aiki da ba su kai 4,000 ba

Ga mata kuwa, yan mataki 13 da sama su sanya 'skirt' da wando ko dogayen kaya da suka rufe gwiwa, The Guardian ta ruwaito wannan.

Wadanda suke mataki na 07-12 kuma za su iya sanya dogayen riguna ko kananan riguna da masu rufe hannu; an hana sanya wadanda ba su da hannu.

An ce mata za su iya sanya kaya na gargajiya ranar Juma’a da lokuta na musamman idan kayan na da tsari mai mutunci.

Gargadin da aka yi ga ma'akata a Delta

Takardar ta gargadi cewa suturar mata ba ta kamata ta nuna kirji ko jawo fitina ba; kuma an hana fitar da surar jiki waje.

An bayyana cewa wannan doka tana da nufin tabbatar da ladabi da bin ka’ida a tsarin suturar ma’aikatan gwamnati a Delta.

An umurci manyan sakatarori da shugabannin sassa su yada sabuwar doka tare da tabbatar da cikakken bin ta a tsakanin ma’aikata.

Gwamna zai fara biyan zaurawa N15,000 a wata

Mun ba ku labarin cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya kaddamar da shirin tallafawa zawara, inda mata 10,000 za au amfana da tallafa duk wata.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi gargadi bayan luguden wutan Isra'ila a Qatar da jiragen yaki

Sheriff Oborevwori ya za a fara biyan kowace bazawara da aka dauka karkashin shirin N15,000 duk wata tare da inshorar lafiya.

Ya ce matan da suka rasa mazajensu ta hanyar mutuwa ko rabuwar aure su na fama da matsin rayuwa da tsangwama daga al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.