Mutuwa Ta Taba Sarakuna, Wamban Dawakin Zazzau Ya Rasu a Gadon Asibiti
- Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya rasa yayansa, Wamban Dawakin Zazzau, Alhaji Aminu Pate
- Masarautar Zazzau ta tabbatar da rasuwar Wanban Dawaki bayan fama da jinya a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello Zaria (ABUTH), Shika
- Rahotanni sun nuna cewa an yi wa marigayin sutura bisa tsarin addinin Musulunci a fadar mai martaba Sarkin Zazzau a yau Alhamis
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zazzau, jihar Kaduna - Masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna ta rasa daya daga cikin sarakunanta a daren jiya Laraba, 10 ga watan Satumba, 2027
Wamban Dawakin Zazzau, Alhaji Aminu Pate ya riga mu gidan gaskiya a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello Zaria (ABUTH) da ke Shika.

Source: Twitter
Masarautar Zazzau ta tabbatar da wannan rasuwa a wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na manhajar X a safiyar yau Alhamis, 11 ga watan Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wamban Dawakin Zazzau ya kwanta dama
Sanarwar da masarautar ta fitar, ta nuna alhini da juyayi tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin da dukkan al’ummar Zazzau baki ɗaya.
Masarautar ta kuma nuna cewa rasuwar Alhaji Aminu Pate babban rashi ne ga masarauta da ma al’ummar jihar Kaduna gaba ɗaya.
Sanarwar ta ce:
"InnalilLahi wa inna ilaihi raji’un. Cike da alhini da miƙa wuya ga ƙaddarar Allah (SWT), Masarautar Zazzau ta na sanar da rasuwar Wamban Dawakin Zazzau, Alhaji Aminu Pate.
"Ya rasu daren jiya (Laraba, 10 ga watan Satumba, 2025) a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Zaria (ABUTH), da ke Shika."
Manyan mutane sun halarci jana'izar basaraken
Jaridar Leadership ta tattaro cewa marigayi Alhaji Aminu Pate, yaya ne ga kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
Rahotonni sun nuna cewa an yi jana'izar marigayi kamar yadda addinin musulunci ya tanada yau Alhamis a fadar mai martaba Sarkin Zazzau.
Cikin manyan bakin da suka halarci jana’izar akwai Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, da tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero.
Shugaban ƙaramar hukumar Zariya, Injiniya Jamil Ahmad Muhammad, yan majalisar masarautar Zazzau, hakimai, masu rike da sarautu, malamai da wasu jiga-jigai sun halarci jana'izar.

Source: Facebook
Iyan Zazzau ya mika sakon ta'aziyya
A cikin sakon ta’aziyya, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana marigayi ɗan uwansa a matsayin “ɗan uwa na amana, uba nagari, mutum mai karamci kum musulmi na ƙwarai."
“Ɗan uwana yana da kima a matsayin jagoran al’umma da addini. Ya kasance abin koyi a bangaren sadaukarwa, karamci, gaskiya da rikon amana, kuma ya zama abin koyi ga matasa masu tasowa," in ji shi.
'Diyar mai martaba Sarkin Katsina ta rasu
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya yi rashin ’yarsa, Khadijah Abdulmumin Kabir Usman , wacce ta rasu a Abuja.
Marigayiya Khadijah, wacce ake kira Andijo, ta kasance abar kauna ga kowa a gidan sarautar, kuma ta rasu ta bar yara uku tana da shekaru 35 da haihuwa.

Kara karanta wannan
Da gaske an kwace sarautar da Sarki ya ba Shugaba Tinubu a Arewa? Gaskiya ta fito
Wannan mutuwa ta jefa masarautar Katsina cikin jimami, inda daruruwan jama’a suka garzaya fadar sarki don yin ta’aziyya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

