NDLEA Ta Kama Wiwi Mai Nauyin Kilo 112 a Wajen Hadarin Mota a Kano
- Jami’an NDLEA sun gano tabar wiwi mai nauyin kilo 112 bayan hadarin mota da ya faru a hanyar Zariya zuwa Kano
- Lamarin ya faru ne bayan direban motar ya yi kokarin guje wa shingen binciken jami'an NDLEA, sai ya yi karo da babbar mota
- An kama mutum daya yayin da yake kokarin tserewa daga motar, kuma direban yana samun kulawar likitoci da amsa tambaya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a jihar Kano sun kama tabar wiwi mai nauyin kilo 112.
Jami'an sun yi wannan kame ne a lokacin da suka kai dauki wajen wani hadarin mota da ya faru a safiyar Asabar, 6 ga Satumba, 2025 a kan hanyar Zariya–Kano, kusa da Gadar Tamburawa.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisa, Adamu Aliyu ya aikata laifi mai girma, kotu ta ayyana nemansa ruwa a jallo

Source: Facebook
Kakakin rundunar, Sadiq Muhammad ya wallafa a Facebook cewa lamarin ya faru da 6:00 na safe inda jami’an NDLEA da ke sintiri suka ji karar hadari tsakanin motar Volkswagen Golf da wata babbar mota.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an NDLEA a Kano sun kai dauki
Sadiq Muhammad ya shaida wa Legit cewa jami’an sun hanzarta zuwa wurin hadarin domin ceto rayuka da kuma duba lafiyar wadanda abin ya shafa.
Ya ce:
"Jami'anmu sun ceto direban da fasinja daga cikin motar, fasinjan ya yi kokarin tserewa amma jami’an suka kama shi."
Da suka yi bincike a cikin motar, an gano katuna 150 da buhuna uku na tabar wiwi da aka auna kuma aka samu jimillar kilo 112.

Source: Facebook
Direban ya bayyana cewa yana aiki a matsayin wakilin mai kayan kuma ya taba kai irin wannan kaya a Kano da wasu jihohi.
Haka kuma ya ce ya bi hannu daya ne da hadarin ya faru domin kaucewa shingen duban NDLEA a lokacin shigarsa Kano.
Hukumar NDLEA ta tsaya kan aniyarta
NDLEA ta bayyana cewa wannan lamari ya hada da manyan laifuffuka biyu: bi ta hannu aro wanda ya haddasa hadari, da kuma fataucin miyagun kwayoyi.
Hukumar ta tabbatar da cewa yanzu haka ana ci gaba da bincike, inda direban ke karbar kulawar likitoci kuma yana amsa tambayoyi.
Rahotanni sun nuna cewa direban babbar motar ya samu karaya, yayin da jami’an suka nuna kwarewa da jajircewa wajen kai dauki, ceton rayuka da kuma gano kwayoyi.
Hukumar ta bukaci al’umma da su guji aikata miyagun laifuffuka, musamman fataucin kwayoyi, tare da ba da rahoto idan an ga wata alama ko motsin da ba a amince da shi ba.
Hukumar ta jaddada kudirinta na ci gaba da farauta da hukunta masu hannu a fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya.
Jami'an NLDEA sun yi kame a Kano
A baya, kun ji cewa Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) sun samu babban nasara bayan kama kwalabe 8,000 na akuskura da ake shirin shiga da shi Kano.
Hukumar ta sanar da cewa ta samu nasarar kamun ne lokacin da aka dakatar da wata tirela daga Legas zuwa Maiduguri da ke kan hanyar Gadar Tamburawa, Zaria–Kano.
Rahoton ya ce masu kayan sun boye muguwar kwayar a cikin tirelar, da kuma tsakanin kekunan Napep, inda aka gina kyakkyawan rufin katako domin ɓoye kwalaben.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

