Najeriya Ta Tattaro Harajin sama da N600bn daga Facebook da wasu Kamfanonin Intanet

Najeriya Ta Tattaro Harajin sama da N600bn daga Facebook da wasu Kamfanonin Intanet

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta samu damar karbar biliyoyin Naira na haraji daga kamfanonin intanet na wajen kasar nan
  • Ta bayyana cewa daga cikin kamfanonin da aka samu kudin harajin ta hannunsu akwai Facebook, Amazaon da kuma Netflix
  • Mathew Osanekwu, mai ba da shawara na musamman kan haraji ga Shugaban Kwamitin Gyaran Dokokin Haraji ne ya fadi adadin da daka tara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta samu damar tattara harajin biliyoyin Naira daga harajin da ta samu ta hannun kamfanonin intanet.

Ta ce ta samu sama da Naira biliyan 600 daga harajin VAT da aka karɓa daga manyan kamfanonin ƙasashen waje da ke samar da ayyuka a Najeriya kamar Facebook, Amazon da Netflix.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi gargadi bayan luguden wutan Isra'ila a Qatar da jiragen yaki

Najeriya ta samu karin kudin haraji daga kamfanonin Intanet
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

The Cable ta wallafa cewa wannan bayani ya fito ne daga Mathew Osanekwu, mai ba da shawara na musamman kan haraji ga Shugaban Kwamitin Gyaran Dokokin Haraji a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Najeriya ta samu karin haraji

The street journal ta ruwaito cewa ce wannan nasara ta samu ne sakamakon sauye-sauyen da aka yi wa dokar VAT.

Ya bayyana cewa sauyin ya bai wa Hukumar Karɓar Haraji ta Ƙasa (FIRS) damar haɗa kamfanonin da ba su da tushe a Najeriya a cikin tsarin haraji.

Mathew Osanekwu ya ce:

“Waɗannan kamfanoni ba na Najeriya ba ne, amma yanzu suna biyan haraji a ƙarƙashin Sashe na 10 na Dokar VAT. An yi masu rijista kuma an naɗa su a matsayin wakilan karɓar haraji."

Ya ƙara da cewa wannan mataki yana daidaita da yadda kasashen duniya ke tafiyar da irin wannan tsari, inda ake karɓar haraji daga irin wadannan kamfanoni.

Gwamnati ta yi karin bayani kan harajin

Kara karanta wannan

Kotun Amurka ta kama tsohon shugaba a NNPCL da cin hanci, zai sha daurin sama da shekaru 10

A yayin taron, Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Dokokin Haraji, Taiwo Oyedele, ya musanta jita-jitar cewa gwamnatin Tinubu tana ƙirƙirar sababbin haraji.

Ya ce ana canza dokoki ne domin rage nauyin haraji ga ma’aikata da masu karamin karfi, tare da tabbatar da daidaito da adalci a tsarin karɓar haraji.

Shugaban ya ce:

“Ba sabon haraji ba ne. Wasu na cewa an ƙirƙiro shi. Ina ƙalubalantar duk wanda ke cewa shugaban ƙasa ya kawo sabbin haraji da ya kawo hujja guda daya."

Oyedele ya kuma tunatar da jama’a cewa a watan Yuli 2023, ƙasa da wata biyu bayan hawansa mulki, Shugaba Tinubu ya sanya hannu a kan umarni guda huɗu da suka dakatar da wasu haraji.

An samu harajin daga Facebook da wasu shafukan intanet
Shuugaban Najeriya a yayin wani taro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Ya bayyana cewa harajin da ake ta muhawara a kai, ba sabon abu ba ne, domin an ƙirƙiro shi ne kafin zuwan wannan gwamnati.

Gwamnatin ta jaddada cewa tana kokarin gyara tsarin haraji ne, ba wai ƙara wa jama’a nauyi ba kamar yadda wadansu su ke hasashe.

Kwamitin haraji ya gana gwamnatin Legaas

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Tsare-Tsaren Kudi da Haraji, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa ta gana gwamnan jihar Legas kan haraji.

Kara karanta wannan

Tinubu: Sai da rajistar haraji za a yi hulda da banki a Najeriya daga 2026

Oyedele ya ce kwamitin ya yi kokarin gudanar da tarukan shawara da hadin gwiwa da gwamnoni a sassa daban-daban na ƙasar, amma sau hudu ana soke tarukan.

Ya bayyana cewa an rubuta wasiku zuwa ga gwamna daya daga kowane yanki na ƙasar, amma a wannan lokacin, babu wanda ya amsa sai gwamna na jihar Legas kadai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng