Sarauniyar Kasar Hausa Ta Kafa Tarihi a Hawan Sallar Gani da Aka Yi a Daura

Sarauniyar Kasar Hausa Ta Kafa Tarihi a Hawan Sallar Gani da Aka Yi a Daura

  • Bikin hawan Sallar gani 2025 da aka gudanar a Daura ta jihar Katsina ya kayatar da al'ummar Hausawa a ciki da wajen Najeriya
  • Sarauniyar kasar Hausa, Lubna Mohammed Gusau na daya daga cikin wadanda suka kayatar da bikin al'adar tare da kafa sabon tarihi
  • A bikin hawan, Lubna Gusau ta shiga cikin tawagar hawan, lamarin da ya ja hankalin yan kallo tare da karawa taron armashi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Daura, jihar Katsina - Sarauniyar Kasar Hausa, Lubna Mohammed Gusau (Ph.D), ta kafa tarihi a shekarar 2025 lokacin bikin Hawan Sallar Gani da aka gudanar a Daura, jihar Katsina.

Sarauniya Lubna ta zama mace ta farko a tarihin ƙasar Hausa da ta shiga cikin wannan gagarumin biki na al’adar malam Babaushe.

Dr. Lubna Muhammad Gusau.
Hoton Sarauniyar kasar Hausa, Dr. Lubna Mohammed Gusau a wurin hawan gani Hoto: Ijaba Photography
Source: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa tun ƙarni da dama da suka shude, Hawan Gani ya kasance ginshiƙi na al’adun Hausawa.

Kara karanta wannan

Tawagar kasar Rasha ta dura Najeriya, ta sauka a jihar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane tarihi Sarauniyar kasar Hausa ta kafa?

Sai dai har zuwa bana, ba a taɓa ganin wata mai rike da sarauta ta shiga cikin jerin gwanon dawakan hawan ba sai a wannan karo da Lubna ta shiga.

Wannan sabon tarihi da Sarauniya ta kafa ya karya doguwar al’ada, tare da buɗe sabon babi a tarihin al’ummar Hausawa.

Da kwarjini da kwalliya ta sarauta, Dr. Lubna Gusau ta kayatar da dubban jama’a, inda bikin ya wuce nuna al’ada kadai, ya koma shaida ta haɗin kai, ci gaba da karfafa gwiwar malam Bahaushe.

Lubna Gusau ta kayatar da mutane a Daura

A lokacin hawan, ta yi ado da launukan sarauta masu ɗaukar ido, tana tafiya cikin kasaita, martaba da girma.

Titunan Daura sun zama abin kayatarwa yayin da dawakai 100 da aka kawata da ado, da rakuma 30 da aka lulluɓe cikin riguna masu haske, suka taka rawa wajen ƙara armashin bikin.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi gargadi bayan luguden wutan Isra'ila a Qatar da jiragen yaki

Wannan shekara ta 2025 za ta shiga cikin tarihi, domin bikin Hawan Gani ya wuce a misalta shi da kyau kadai, ya zama alamar ci gaba, alfahari da raya al’adu a ƙarƙashin haske da adon Sarauniya, Dr. Lubna Mohammed Gusau.

Dr. Lubna Muhammed Gusau.
Hoton Sarauniyar Kasar Hausa a wurin hawan gani a Daura Hoto: Ijaba Photography
Source: Facebook

Muhimman abubuwan da aka lura a bikin

  • Mataki na tarihi: Dr. Lubna Mohammed Gusau ta zama mace ta farko da ta shiga cikin Hawan Gani.
  • Darajar al’adu: Bikin ya nuna ƙarfin al’adun Hausawa da haɗin kai.
  • Kwarjini: Sarauniya ta kara fito da ɗaukaka da mutuncin sarauta.
  • Kayatarwa: Dawakai 100 da rakuma 30 da aka kawata sun ƙara armashi da kyaun bikin al'adar.
  • Tasiri: Bikin ya zama alamar ci gaba, alfahari da kuma raya al’adun malam Bahaushe.

Sarkin Daura ya ba uwargidan gwamna sarauta

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Sarkin Daura da ke jihar Katsina ya nada Hajiya Zulaihat Dikko Radda a matsayin Jagaban Matan Hausa.

Hakan ya sa Hajiya Zulaihat, uwar gidan gwamnan jihar Katsina ya zama ta farko da aka ba wannan sarauta a kasar Hausa.

Sarkin ya bayyana cewa an ba Hajiya Zulaihat wannan sarauta ne saboda jajircewarta wajen tallafawa mata musamman a bangaren ƙarfafa su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262