Shugaba Tinubu Zai Yi Jawabi Kai Tsaye ga 'Yan Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta fara shirya bukukuwan da za a yi a ranar 1 ga watan Oktoban 2025, watau ranar samun yancin kai
- Daya daga cikin abubuwan da aka tsara za a yi a ranar 'yancin shi ne jawabin shugaban kasa, Mai girma Bola Ahmed Tinubu
- Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya kaddamar da kwamitin da zai jagoranci shirya bukukuwan wannan rana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi kai tsaye ga al’ummar Najeriya a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025.
Jawabin da shugaban kasa Tinubu zai yi na cikin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta yi na bukukuwan cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

Source: Facebook
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin kaddamar da kwamitin IMC a Abuja, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan
'Sau 2 ba mu sallar Juma'a': Musulmai sun roki sauya ranar nadin Sarki da za a yi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kaddamar da kwamitin bikin ranar yanci
Kwamitin IMC, wanda ya kunshi ministoci shi ne zai shirya duka bukukuwan da za a yi domin murnar zagayowar ranar da Najeriya ta samu yanci daga turawan mulkin mallaka.
Akume ya bayyana cewa an ɗora wa kwamitin alhakin tsarawa, shiryawa da aiwatar da duk shirye-shiryen da aka amince da su domin bikin ranar tunawa da samun ‘yancin kai.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya fitar, jiya Laraba.
Abubuwan da ranar yanci ke tunawa 'yan Najeriya
Ya bayyana ranar tunawa da samun ‘yanci a matsayin wani lokaci na farin ciki da kuma nazari kan nasarorin da aka samu da kuma inda aka dosa.
"Wannan bikin na tuna mana inda muka fito da kuma inda muka nufa a matsayin ƙasa. Najeriya ta fuskanci ƙalubale a fannoni daban-daban, siyasa, tattalin arziki da zamantakewa, amma ta tsallake su.
"Biki irin wannan ba wai na murnar abin da ya gabata kaɗai ba ne, amma har da tunani kan matakan nan gaba.”
- Geroge Akume.
Jawabin Tinubu da sauran shirye-shirye
Bisa ga jadawalin da gwamnati tarayya ta fitar, bukukuwan za su fara da taron manema labarai na duniya a ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025.
A ranar Jumma’a, 26 ga Satumba, za a gudanar da sallar Juma’a tare da addu'o'i ga kasa, sannan za a yi wasu shirye-shiryen mata.
A ranar Asabar, 27 ga Satumba, za a gudanar da tarukan matasa da kuma nuna tarihi da fasaha, cewar rahoton Punch.

Source: Facebook
Ranar Lahadi, 28 ga Satumba, za a yi ibadar Coci, sannan a ranar Litinin, 29 ga Satumba, za a gudanar da muhawara ta musamman.
Bikin zai kara armashi da jawabin Shugaban Ƙasa Tinubu da kuma faretin murnar samun ‘yancin kai a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025.
Tinubu ya dauki matakin rage farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gaggawa na sauke farashin abinci domin saukakawa 'yan Najeriya.
Umarnin ya mayar da hankali ne wajen tabbatar da tsaro da saukin jigilar kayan gona a manyan hanyoyi domin rage kudin sufuri.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da 'yan kasa ke kara kokawa kan yadda abinci ke lakume kaso mafi tsoka na albashinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

