Ina Suka Makale? An Ji Abin da Ya Hana Tallafin N50,000 Isa ga Mutane a Kano

Ina Suka Makale? An Ji Abin da Ya Hana Tallafin N50,000 Isa ga Mutane a Kano

  • Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa duka matan da aka zaba domin cin gajiyar tallafin N50,000 za su samu hakkinsu nan ba da jimawa ba
  • Kwamishinar matan Kano, Hajiya Amina Sani ce ta bayyana hakan bayan korafe-korafe sun fara yawa daga mata masu cin gajiyar shirin
  • An bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su ci gaba da tallafawa mata domin su koyi sana'o'in dogaro da kansu a kananan hukumomin Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kwantar da hankulan matan da aka dauki sunayensu da nufin ba su tallafin N50,000 amma har yanzu ba su karbi kudin ba.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa duka mata marasa galihu da masu rauni a aka zaba karkashin wannan shirin, za su karbi tallafin kudin nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Kungiyar dattawan Arewa ta samo.mafita ga gwamninin yankin

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Kwamishinar harkokin mata ta jihar Kano, Hajiya Amina Sani Abdullahi ce ta fadi hakan da take hira da yan jarida a taron haska fim da aka shirya a Kano, cewar rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya hana mata samun tallafin N50,000?

Da take bayani kan abin da ya sa tallafin bai kai ga matalautan matan ba, Amina Sani ta ce matan suna da yawa matuka, amma a hankali tallafin zai isa gare su.

Kwamishinar, wacce Daraktan bincike da tsare-tsare na ma’aikatar, Yakubu Muhammad, ya wakilta, ta bayyana cewa akwai korafe-korafe daga jama’a saboda wasu ba su samu tallafin ba.

“Tun da gwamnati ce ke gudanar da wannan shiri, babu shakka tsammanin jama’a zai yi yawa, musamman ma saboda yawan mata da aka ware wa tallafin suna da yawa matuƙa.
"Hakan ne ya sa wasu ke cewa ba a kai musu ba. Duk da haka, ana ci gaba da ƙoƙari don tabbatar da cewa kowa ya samu.”

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan lokacin fara biyan harajin fetur

Hajiya Amina ta yaba da ƙoƙarin kungiyoyin Fable Advisory and Isa Wali Empowerment Initiative bisa yadda suke taimaka wa gwamnati wajen tabbatar da cewa mata sun samu ƙarfin gwiwa da damar dogaro da kai.

An nemi gwamnati ta tallafawa mata a Kano

A nata ɓangaren, Amina Hanga wacce ita ce Daraktar gudanarwa ta Fable Advisory and Isa Wali Empowerment Initiative, ta nuna farin cikinta da sakon da fim ɗin ya isar.

Ta kuma kara da kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da a ba mata damar shiga harkokin kasuwanci.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hoton Gwamna Abba Kabir a wurin taron da ya shafi mata a Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen tallafawa shirye-shiryen raya mata a jihar, tana mai cewa:

“Muna farin cikin ganin saƙon ya isa, kuma da alama an karɓe shi hannu biyu duba da maganganun masu kallon da suka mahalarta.
"Wannan hanya ce ta ƙarfafa mata a cikin al’umma, tana kuma buɗe hanyoyi da damarmaki. Ya kamata mu ƙarfafa mata su koyi sana’o’i da ƙwarewa domin rage wahalhalu a cikin iyalai."

Mahajjacin Kano ya bata a Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da batan daya daga cikin mahajjatan Kano yayin aikin hajjin 2025 a kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun badda kama yayin tafka ta'asa a Zamfara

Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa da Saudiyya na aiki kafada da kafada wajen gano mahajjacin tare da dawo da shi gida cikin iyalansa.

Amirul hajj na Kano na bana 2025 kuma Sarkin Karaye, Alhaji Muhammadu Maharaz ya mika rahoton abubuwan da suka faru a aikin hajji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262