Barayi Sun Addabi Neja, Gwamna zai Zauna da 'Yan Bola Jari a Gidan Gwamnati

Barayi Sun Addabi Neja, Gwamna zai Zauna da 'Yan Bola Jari a Gidan Gwamnati

  • Gwamna Muhammad Umaru Bago ya ce gwamnati ba za ta amince da masu fakewa da bola jari su ci gaba da satar kayayyaki ba
  • A karkashin haka, gwamnan Neja ya bukaci shugabannin ƙungiyar su tantance mambobinsu tare da gano masu laifi a cikinsu
  • Za a yi babban taro tare da hukumomin tsaro da shugabannin ƙungiyar na kananan hukumomi 25 na jihar Neja don neman mafita

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja – Gwamnatin Neja ta gudanar da muhimmin taro da shugabannin ƙungiyar ’yan bola jari domin kawo karshen matsalar lalata kadarori da satar kayayyakin gwamnati da na jama'a.

Taron ya gudana ne a fadar gwamnatin jihar da ke garin Minna, bisa jagorancin Gwamna Umaru Bago.

Gwamna Bago a wani taro a majalisar zararwar Neja
Gwamna Bago a wani taro a majalisar zartarwar Neja. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Twitter

Legit.ng Hausa ta tattaro bayanai kan yadda aka yi zaman ne a wani sako da aka wallafa a shafin gwamnan na Facebook.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun dawo shiga jama'a, kasuwa da asibiti a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bago ya nuna damuwarsa kan yadda ake ci gaba da ganin barayi na fakewa da suna ’yan bola jari suna satar kayayyaki daga gine-gine da wuraren gwamnati da na jama’a.

Ya ce gwamnati ba za ta zauna shiru ba yayin da wadannan miyagu ke ci gaba da barna, tare da bukatar shugabannin ƙungiyar su dauki matakin gaggawa wajen tsarkake ƙungiyarsu.

Gwamna Bago ya ba 'yan bola jari shawari

Gwamna Bago ya shawarci shugabannin ’yan bola jari su fito da tsarin tantance membobi domin a san masu gaskiya da kuma fitar da baragurbi.

Ya ce dole ne a samar da tsarin da zai tabbatar da cewa duk wanda ya shiga harkar ba zai rika aikata barna ba.

Gwamnan jihar Neja ya gayyaci 'yan bola jari

Ya kara da cewa za a shirya wani babban taro da zai hada shugabannin ƙungiyar daga kananan hukumomi 25 tare da hukumomin tsaro domin nazarin sabbin dokokin aiki.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kawo tsarin aiki da ba a taba yi ba a Najeriya, komai zai sauya a ofisoshi

Gwamnan ya ce idan bukatar hakan ta taso, za a gabatar da kudirin doka a gaban majalisar dokokin jihar domin tabbatar da an hukunta masu karya ka’ida.

An gayyaci shugabannin bola jarin ne daga dukkan kananan hukumomi 25 a jihar zuwa babban taro a ranar Talata, 16 ga Satumba, 2025, da misalin karfe 10:00 na safe.

Gwamnan jihar Neja yana wani jawabi
Gwamnan jihar Neja yana wani jawabi. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Bago ya ba 'yan bola jari shawari

Gwamnan ya umarci rundunar sa ido ta ƙungiyar da ta kara himma wajen aiki musamman a manyan hanyoyin shiga da fita daga jihar domin dakile 'yan bola jarin da ba su da lasisi.

Umaru Bago ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama da laifi za a hukunta shi bisa doka ba sani ba sabo.

Martanin shugabannin ’yan bola jari

Shugaban ƙungiyar a jihar, Malam Mohammed Ahmed, ya bayyana cewa suna shirin bullo da tsarin samar da tufafi da kuma katin shaida ga mambobi domin rage damfara da sata.

Ya gode wa Gwamna Bago bisa wannan zama, tare da neman goyon bayan gwamnati domin cimma burin hana saye da sayar da kayan sata a jihar.

Kara karanta wannan

Hakurin matasa ya fara karewa, sun yi barazanar yin gaba da gaba da 'yan bindiga

Gwamnatin Bago ta karyata hana wa'azi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta sanar da cewa ba daga wajenta aka samu labarin saka dokar wa'azi ba.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban hukumar addini ne na jihar ya fitar da sanarwar bayan wani taro da ya kira.

A bayanin da hukumar ta fitar a karon farko, ta bayyana cewa za a bukaci kowane malami ya yi rajista kafin ya yi wa'azi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng