Sojoji Sun Samu Nasara kan 'Yan Bindigan da Su Ka Shirya Ta'asa a Katsina
- Dakarun sojoji tare da ’yan sanda da jami’an tsaro na C-Watch sun fatattaki wasu ’yan bindiga a jihar Katsina
- ’Yan bindigan sun kai hari ne kauyukan Gago da Ruwan Dorawa, inda su ka sace mutane tare da jikkata wasu bayin Allah
- Rundunar sojoji ta bayar da tabbacin cewa za a ci gaba da sintiri don dawo da zaman lafiya a yankin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina – Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma tare da hadin gwiwar ’yan sanda da kuma jami’an tsaro na C-Watch, sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina.
Dakarun sojojin sun fatattaki ’yan bindigan ne bayan da su ka kai wani hari a karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro da ƴan bindiga sun gwabza ƙazamin faɗa a Malumfashi, an rasa rayuka
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru da safiyar ranar Talata, 9 ga watan Satumban 2025, lokacin da ’yan bindiga suka afka kauyukan Gago da Ruwan Dorawa.
'Yan bindigan sun yi garkuwa da mutane biyu, Labaran Jalli mai shekaru 35 da Umma Sabon Gero mai shekaru 30, tare da jikkata wasu.
Mutane sun samu raunuka a harin
Hakazalika, 'yan bindigan sun raunata wani mutum tare da jami'an rundunar C-Watch a yayin harin.
Daga cikin wadanda aka raunata akwai wani mazaunin kauyen Gago, Labiru Umaru mai shekaru 40, da kuma jami’an tsaro na C-Watch guda biyu, Abba Mohammed mai shekaru 30 da Suleman Shuaibu mai shekaru 35.
Dakarun sojoji sun kai dauki
Sai dai, hanzarin sojoji tare da hadin gwiwar ’yan sanda da jami’an tsaron C-Watch sun isa wurin, inda su ka fafata da ’yan bindigan, sannan su ka tilasta musu janyewa.
An garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibitin gwamnati na Dutsinma domin samun kulawar likitoci, yayin da ake ci gaba da kokarin kamo wadanda suka aikata laifin da kuma ceto mutanen da aka sace.

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Rundunar ta tabbatar wa mazauna yankin cewa sojojin Operation Fansan Yamma tare da sauran jami’an tsaro za su ci gaba da gudanar da sintiri domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Source: Facebook
Karanta wasu karin labaran kan sojoji
- Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka
- Jami'an tsaro da ƴan bindiga sun gwabza ƙazamin faɗa a Malumfashi, an rasa rayuka
- 'Yan bindiga sun shiga uku, gwamna zai gina sabon sansanin sojoji na musamman a Kebbi
- Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga bayan an yi gumurzu a Katsina
'Yan bindiga sun yi barna a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kwashe kwanaki uku suna kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kashe mutane tare da yin awon gaba da wasu masu yawa a hare-haren da suka kai a kauyukan da ke karamar hukumar Sabuwa.
Mazauna yankin sun mika kokensu ga gwamnati kan ta kawo musu dauki daga irin barnar da 'yan bindigan suke yi musu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng