Sojoji da 'Yan Bindiga Sun Gwabza Kazamin Fada a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

Sojoji da 'Yan Bindiga Sun Gwabza Kazamin Fada a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

  • 'Yan bindiga sun shirya harin kwanton bauna kan dakarun sojoji masu yi wa 'yan kasuwa rakiya a jihar Zamfara
  • Lamarin ya jawo an yi musayar wuta mai zafi a tsakanin bangarorin biyu, wadda ta jawo asarar rayuka
  • Harin ya kuma ritsa da fasinjojin cikin motocin wadanda suka samu raunuka bayan sun samu kansu a tsakiyar musayar wuta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Dakarun sojoji masu aikin samar da tsaro da 'yan bindiga sun gwabza fada a jihar Zamfara.

Akalla sojoji biyar da kuma ‘yan bindiga da dama ne suka mutu yayin artabun da aka yi a tsakanin bangarorin biyu.

Sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga a Zamfara
Hoton shugaban sojojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, yana jawabi ga jami'an tsaro Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa sojojin da 'yan bindigan sun yi artabun ne a kan hanyar Lilo-Gulubba da ke karamar hukumar Gusau, jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce dakarun sojojin suna rakiyar ‘yan kasuwa ne zuwa kasuwar Gusau lokacin da wata tawagar ‘yan bindiga masu yawa ta yi musu kwanton bauna.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun boye ne a gefen hanya, inda daga bisani suka fito kwatsam suka fara harbi kan jerin motocin.

Yadda sojoji suka fafata da 'yan bindiga

Wani ganau ba jiyau, Mohammed Isa, ya ce fasinjoji da dama sun tsere don tsira da rayukansu.

"An samu rikici sosai, fasinjoji sun tsere cikin daji don tsira, yayin da sojoji suka mayar da martani cikin gaggawa, su ka rika musayar wuta da ‘yan bindigan."

- Mohammed Isa

A cewarsa, a yayin musayar wutar, sojoji biyar sun mutu tare da wasu ‘yan bindiga da dama.

Haka kuma, wasu daga cikin fasinjoji sun samu raunuka kuma an garzaya da su zuwa babban asibitin Kotorkoshi domin jinya.

Mohammed Isa ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Harin 'Yan Boko Haram ya fusata sojoji, sun hallaka tsageru masu yawa a Borno

“Muna kan hanyar zuwa Gusau tare da rakiyar sojoji, sai ga ‘yan bindigan da su ka boye sun fito suna kai mana hari."
"Sojojin sun yi kokari sosai wajen mayar da martani, suka kashe da dama daga cikin ‘yan bindigan. Amma abin bakin ciki, sojoji biyar sun rasa rayukansu."
"Wasu fasinjoji sun ji rauni sosai, amma da yawa daga cikinmu mun tsira lafiya. Da ‘yan bindigan suka ga sun fara fuskantar rashin nasara, sai suka ja da baya suka koma maboyarsu.”
Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An ji ta bakin sojoji kan harin

Da aka tuntubi jami’in yaɗa labarai na rundunar sojoji, Kyaftin David Adewusi, ya ce bai samu rahoton lamarin ba tukuna, amma ya yi alkawarin zai bayar da bayani daga baya.

"Ban samu wannan labari ba tukunna, amma zan kira daga baya."

- Kyaftin David Adewusi

Sai dai har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoton, bai bayar da karin bayani ba.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Katsina, an tura miyagu zuwa barzahu

'Yan bindigan sun hallaka mutane tare da yin awon gaba da wasu da dama a harin da suka kai a karamar hukumar Faskari.

Mutanen yankin sun koka kan janye jami'an tsaro, inda suka nuna cewa hakan ya sanya suna fuskantar hare-hare.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng