DSS Ta Shiga tsakani, Ta Kawo Karshen Sabanin NUPENG da Kamfanin Dangote
- Hukumar tsaron kaya ta DSS ta samu nasarar kawo karshen yajin aikin NUPENG kafin ya jawo matsala ga 'yan Najeriya
- DSS ta sulhunta rikici tsakanin kamfanin Dangote da NUPENG bayan an yi wani zaman sirri a Abuja, kuma an shawo kan matsalar
- NUPENG ta tsunduma yajin aiki ne saboda zargin kamfanin Dangote da kanainaye bangaren sufuri da rarraba man fetur
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta shiga tsakani domin kawo karshen sabanin da ya kunno kai tsakanin kamfanin Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas (NUPENG).
DSS ta cimma nasara bayan wani taron sirri da aka gudanar a hedikwatar DSS da ke Abuja, inda aka cimma matsaya, NUPENG ta dakatar da yajin aikin da ta fara a Najeriya.

Source: Getty Images
Daily Trust ta ruwaito cewa Ministan Kudi, Wale Edun; Ministan Kwadago da Ayyuka, Mohammed Maigari Dingyadi; da Ministar Ƙasar Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha sun halarci taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran wadanda su ka halarci taron sun hada da Babban darektan kamfanin Dangote, Alhaji Sayyu Dantata, wanda ya jagoranci tawagar kamfanin.
NUPENG ta zauna da DSS, wakilan kamfanin Dangote
Jaridar Punch ta wallafa cewa Shugaban NUPENG, Akporeha Williams da Sakatare Janar, Olawale Afolabi, da wakilan NLC da TUC suma sun halarci taron.
A cewar wani jami’in tsaro, shugaban kasa Bola Tinubu ne ya ba da umarni kai tsaye ga Shugaban DSS, Oluwatosin Ajayi da sauran jami'ansa su tabbata yajin aikin bai jawo matsalar man fetur ba.
Bayan tattaunawa mai tsawo da ta ɗauki kusan awa shida, an cimma yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu inda kamfanin Dangote ya amince ma’aikatansa su samu damar shiga ƙungiyar NUPENG idan suna so.

Source: Getty Images
Amma dai ba za a tilasta wa kowa shiga ba, domin dokokin ƙasa sun baiwa kowane ma’aikaci ’yancin zaɓin abin da ya ke ganin ya fi masa alheri.
An cimma yarjejeniya tsakanin NUPENG da Dangote
Yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kanta ta kunshi cewa za a fara tsarin hadewa da ƙungiyar daga ranar Talata, 9 ga Satumba, 2025 zuwa Litinin, 22 ga Satumba, 2025.
Haka kuma, Dangote ba zai kirkiro wata sabuwar ƙungiyar da za ta zama kishiya ga NUPENG ko PENGASSAN ba.
Bayan cimma matsaya, NUPENG ta sanar da dakatar da yajin aikin gaba ɗaya. Shugaban ƙungiyar, Akporeha, ya bayyana hakan a matsayin nasara ga ma’aikata da talakawan Najeriya.
Ya ce:
“Mun yi nasara. Komai ya koma daidai. An rattaba hannu kan yarjejeniyar. Godiya ga dukkannin masu goyon baya."
Kungiyar NUPENG ta shiga yajin aiki
A wani labarin, mun wallafa cewa Kungiyar NUPENG ta bayyana damuwarta bisa ikirarin cewa matatar Dangote na kokarin karya tsarin dake tsakanin masu dakon man fetur.
A gefe guda, NUGASA, kungiyar masu gidajen mai da iskar gas ta kasa ta bayyana cikakkiyar goyon bayanta ga NUPENG sannan ta zargi kamfanin Dangote da kokarin kawo masu cikas.
IPMAN, kungiyar dillalan fetur, ta yi kira da a sasanta rikicin cikin lumana, ta bukaci a zauna a teburin sulhu domin tabbatar da wadatar man ba tare da tashin farashi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


