Duk da Fara Shirin Sulhu, 'Yan Bindiga Sun Yi Kisa, Sn Sace Mutane Masu Yawa a Katsina
- 'Yan bindiga sun yi ta'asa baya sun kai wani harin ta'addanci a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina
- Miyagun 'yan bindigan sun farmaki wani kauye wanda ya shafe shekara 10 yana fuskantar hare-hare, inda suka kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu
- Rundunar 'yan sandan jihar ta bayar da tabbacin cewa tuni ta fara gudanar da bincike domin zakulo masu hannu a mummunan lamarin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jhar Katsina - ‘Yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutane uku a wani hari da suka kai a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Kadisau da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, da yammacin ranar Litinin.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce maharan sun bar jama’a da dama cikin raunuka, inda aka garzaya da su zuwa asibitoci na kusa domin samun magani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun sace mata da yara
Mutanen yankin sun bayyana cewa an yi garkuwa da mata da yara da ba a san adadinsu ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa kimanin mutane huɗu daga cikin waɗanda aka sace, an riga an sanya musu rana kuma an shirya za su yi aure kafin karshen shekarar 2025.
Kauyen Kadisau ya sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan shekarun nan. Wannan sabon hari shi ne na biyu cikin kwanaki 10.
Mafi munin harin da aka kai a kauyen ya faru a shekarar 2019, lokacin da aka kashe mutane sama da 70.
Mutane sun koka da janye jami'an tsaro
Mazauna yankin sun bayyana fushinsu kan janye dakarun tsaro kwatsam daga yankin, abin da suka ce ya bar su cikin hali na rauni da rashin kariya.
Sun roƙi gwamnati da ta gaggauta ta sake mayar da dakarun tsaro domin hana ci gaba da kai hare-hare tare da dawo da zaman lafiya.
Shaidu sun bayyana cewa mutane da dama, musamman mata da yara, sun fara tserewa daga kauyen tun misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Litinin bayan harin.
'Yan sandan Katsina sun yi bayani
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadik Aliyu, ya tabbatar da cewa ana gudanar da bincike.

Source: Twitter
Ya kuma tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna kara kaimi wajen bin diddigin waɗanda suka kai harin.
Kakakin 'yan sandan ya yi gargaɗin cewa karshen mutanen banza da ke addabar jama’ar jihar Katsina masu son zaman lafiya, ya kusa zuwa.
'Yan bindiga sun sace mutane a zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda sun yi basaja wajen kai hari a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
'Yan ta'addan sun yi shiga irin ta mata inda suka sanya hijabai da rigunan mama don badda kama wajen sace mutane a garin Dansadu.
Tantiran sun yi awon gaba da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, duk da kokarin da jami'an tsaro suka yi na bin bayansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

