Majalisa na Barazanar Hada Minista da Tinubu kan 'Raina' 'Yan Najeriya da Suka Yi Hadari
- Kwamitin harkokin sufurin ƙasa na Majalisar Wakilai ya ba Ministan sufuri, Sa’idu Alkali sa'o'i 48 ya bayyana a gabansa
- ‘Yan majalisa sun nuna bacin rai kan rashin halartar taron bincike kan hatsarin jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna
- Sun ce rashin zuwan ministan ya nuna gazawa da raina al’umma, tare da yin gargadin kai rahoto kai tsaye ga shugaban ƙasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da sufuri ya yi tir da rashin halartar Ministan sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali, a taron bincike kan hatsarin jirgin ƙasa na Abuja–Kaduna.
A watan da ya wuce ne aka yi hadarin jirgin kasa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna kuma ya rutsa da fasinjoji da dama.

Source: Facebook
The Guardian ta wallafa cewa kwamitin ya bayyana bacin rai kan abin da ya kira raina al’umma, inda ya ce rashin halartar ministan ya nuna gazawa da rashin mutunta majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabar kwamitin, Blessing Onuh, ta bayyana cewa rashin zuwan ministan abin kunya ne a lokacin da al’ummar ƙasar ke neman amsoshin gaskiya kan hadarin.
Minista ya ki bayyana a Majalisar tarayya
Blessing Onuh ta ce mambobin kwamitin sun bar hutu, wasu ma daga Lagos, domin gudanar da binciken, amma abin takaici ministan ya ƙi bayyana.
A cewarta:
“Mun dakatar da zaman nan har sai ya bayyana cikin sa'o'i 48. Rayukan ’yan Najeriya sun shiga haɗari, ba wasa ake yi ba.”
Onuh ta ƙara da cewa dole ne majalisa ta tsawatar kan hadarin da ya faru, domin jama’a sun cancanci su bayani kan irin barazanar da fasinjojin suka shiga.
'Yan majalisa sun gargadi Ministan sufuri
Tribune ta rahoto cewa mataimakin shugaban majalisar, Philip Agbese, ya bayyana rashin halartar ministan a matsayin shaida ta rashin kwarewa da kuma raina ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan
Kungiyar TUC ta ja daga, ta ba gwamnatin Tinubu kwanaki 14 ta janye harajin fetur
Ya ce:
“Wannan mataki ya nuna ba shi da cancantar gudanar da aikin da shugaban ƙasa ya dora masa. Idan ya ƙi bayyana, jama’a su sani cewa Ministan sufuri bai aiki a ƙasar nan.”
Agbese ya tunatar da gargadin shugaban ƙasa cewa babu wani minista ko shugaba da ya kamata ya raina majalisa, amma Alkali ya nuna rashin girmamawa shugabanci.

Source: Facebook
Maganar sauran ‘yYan majalisar wakilai
Wani mamba na kwamitin, Cyril Hart, ya nuna takaici kan yadda Alkali, wanda shi ma tsohon ɗan majalisa ne, ya nuna rashin mutunta majalisar.
Hart ya ce:
“Mutane 618 sun fuskanci barazanar rasa rayuka. Wannan abin damuwa ne a tsarin tsaron hanyoyin jirgin ƙasan mu. Yadda minista ya ki bayyana cin amanar al’umma ne.”
'Yan majalisar sun yi gargadin cewa idan ya ci gaba da ƙin girmama kiran majalisa, za su aika da rahoto kai tsaye ga shugaban ƙasa domin ɗaukar mataki.
Majalisa ta hana Sanata Natasha dawowa
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta gargadi Sanata Natasha Akpoti da cewa kar ta kuskura ta ce za ta dawo aiki.
Hakan na zuwa ne bayan Sanatar ta kammala wa'adin wata shida na dakatar da ita da aka yi bayan wani sabani da suka yi.
Majalisar ta bayyana cewa lamarin yana gaban kotu kuma dole sai alakali ya yanke hukunci za su dauki mataki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

