Meya Sa Rubutun Sowore Ya Fusata DSS? Muhimman Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani
A karshen makon jiya ne rikici ya barke tsakanin hukumar tsaro ta DSS da fitaccen dan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore kan sukar da ya yi wa Shugaba Bola Tinubu.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
DSS ta nuna bacin ranta kan kalaman da Sowore ya yi amfani da su wajen sukar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, lamarin da ya sa ta fara yunkurin goge rubutun.

Source: Twitter
A sanarwar da ta wallafa a shafinta ranar Asabar, 6 ga watan Satumba, 2025, DSS ta bukaci dandalin sada zumunta na X ya gaggauta goge rubutun Sowore kuma a rufe shafinsa gaba daya.
A cewar DSS, ta dauki wannan matakin ne bisa zargin Sowore da amfani da shafinsa wajen yaɗa bayanai na ƙarya da cin mutunci da kuma kalaman da za su iya tayar da rikici a ƙasa.

Kara karanta wannan
Da gaske an kwace sarautar da Sarki ya ba Shugaba Tinubu a Arewa? Gaskiya ta fito
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar hukumar, kalaman Sowore sun zama barazana ga tsaron ƙasa kuma ba karamin cin mutunci ba ne ga mutum mai girma kamar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ko me Sowore ya fada da ya fusata DSS?
Tun farko dai Sowore ya soki Shugaba Tinubu kan maganar da ya yi lokacin ziyarar da ya kai kasar Brazil cewa gwamnatinsa ta kakkabe cin hanci da rashawa.
Sowore ya rubuta a X cewa: “Wannan mai laifin @officialABAT ya tafi Brazil yana cewa babu cin hanci a gwamnatinsa. Wace irin ƙarfin guiwa ne ya sa shi yin wannan ƙarya ba tare da jin kunya ba?”
Wannan batu ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda magoya bayan Tinubu da wasu ‘yan Najeriya suka rika caccakar Sowore, lamarin da DSS ta ce na iya haifar da tashin hankali.
DSS: Kalaman sun saɓa dokoki
DSS ta lissafa abin da ta kira laifuffuka a cikin kalaman dan gwagwarmayar, waɗanda suka haɗa da:
- Yaɗa bayanai da za su iya tayar da zaune tsaye da ɓata sunan mai girma shugaban kasa.
- Cin mutunci da zai iya ɓata martabar Najeriya a idon ƙasashen waje.
- Wata irin ƙarya da ka iya tayar da ƙiyayya tsakanin al’umma.
Hukumar DSS ta kara da cewa hakan ya saba wa sashe na 51 na dokar hukunta masu laifi da kuma dokokin laifukan intanet na 2025, da kuma dokar hana ta’addanci ta 2022.
“Babu shakka kalaman da Mista Omoyele Sowore ya yi cike suke da karya da cin mutunci da kuma nufin yada wata akida wacce za ta iya haifar da kiyayya, rikici da bata sunan shugaban kasa idon duniya," in ji DSS.
Meya sa DSS ta nemi rufe shafin Sowore?
DSS ta yi nuni da cewa barin Sowore ya ci gaba da amfani da X wajen yaɗa irin waɗannan kalamai zai ƙara haifar da rikice-rikice, cin mutuncin shugaban kasa da bata sunan Najeriya.
Saboda haka ne hukumar tsaron ta bukaci a rufe shafinsa gaba daya domin a ganinta hakan zai dakatar da aikata abin da ya saba doka kamar dai wanda ya yi.

Source: Twitter
Har ila yau, DSS ta ce daukar wannan mataki na rufe shafin Sowore ko dakatar da shi zai dakile yada irin wadannan kalamai masu hadari ga zaman lafiyar Najeriya.
Sai dai masana na ganin wannan mataki zai iya zama yunƙurin murƙushe ‘yancin faɗar albarkacin baki, kasancewar Sowore ya shahara wajen amfani da kafafen sada zumunta wajen sukar gwamnati, in ji rahoton BBC Hausa.
Takaitaccen bayani kan Omoyele Sowore
An haifi Omoyele Sowore a ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar 1971 a yankin Neja Delta da ke Kudancin Najeriya, amma shi dan asalin garin Ese-Odo ne a jihar Ondo.
Sowore ya karanta ilmin wurare a Jami'ar Legas daga 1989 zuwa 1995, inda sau biyu ana korarsa kafin kammala digirinsa na farko saboda dalilai na siyasa da gwagwarmayar dalibai.
Sowore fitaccen dan gwagwarmaya ne kuma ɗan jarida, wanda ke fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, shi ne ya kafa jaridar Sahara Reporters.

Source: Twitter
Dan gwagwarmayar ya nemi takarar shugaban ƙasa a zabukan 2019 da 2023 karkashin inuwar jam'iyyar da ya kafa AAC, in ji rahoton Premium Times.
Hukumomin tsaro sun sha kama Sowore bisa zarge-zarge daban-daban, daga ciki akwai tsare shi da aka yi a 2019 kan shirya zanga-zangar RevolutionNow, in ji rahoton Sahara.
Lauyan Sowore ya soki bukatar hukumar DSS
A wani rahoton, kun ji cewa lauyan dan gwagwarmaya, ya soki bukatar da hukumar DSS ta shigar kan shafin Omoyele Sowore.
A cewar lauyan Sowore, Inibehe Effiong bukatar ba ta da tushe a tsarin doka, kuma idan aka amince da ita, za ta yi mummunan tasiri kan dimokuradiyyar Najeriya.
Ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai kai karar Sowore kotu ba, don haka babu hujja ga DSS ta tsoma baki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


