Rashin Tsaro: Dattawan Arewa Sun Samo Mafita ga Gwamnonin Yankin
- Wata kungiyar dattawan Arewa ta ba gwamnonin yankin shawara kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- Ta bayyana cewa ya fi kyau a ceto rayuwar mutane fiye da kashe kudi masu kauri wajen zuwa yin ta'aziyya
- Kungiyar ta nuna cewa yin sulhu da 'yan ta'adda ba gazawa ba ne, face wata hanya ce da za a kare rayukan jama'a
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wata kungiyar dattawan Arewa mai suna 'Northern Elders Progressive Group' ta yi kira ga gwamnonin Arewa maso Yamma da su shiga tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga.
Kungiyar ta bayyana cewa ya fi kyau a kashe kuɗin jihohi wajen ceton rayuka fiye da zuwa yin ziyarar ta’aziyya.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai kula da yankin Arewa maso Yamma na kungiyar, Mallam Yusuf Abubakar, ya fitar a Sokoto, ranar Talata, 9 ga watan Satumban 2025.
Dattawan Arewa sun ce an samu tsaro
Mallam Yusuf Abubakar ya ce kungiyar ta gamsu da matakan sulhu da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da sauran masu ruwa da tsaki ke ɗauka don dawo da zaman lafiya.
"Muna farin ciki da matakan da ake ɗauka zuwa yanzu. A kwanan nan da na yi tafiya daga Sokoto zuwa Gusau, daga Funtua zuwa Zaria, na lura an samu zaman lafiya fiye da baya."
"An samu ci gaba a harkar tsaro, a aikin sintiri, da kuma tsaron matafiya a kan hanya.”
- Mallam Yusuf Abubakar
Wace shawara aka ba gwamnonin Arewa?
Ya yi kira ga gwamnonin yankin da su rungumi tattaunawa, yana jaddada cewa hakan ya fi tasiri fiye da yawan zuwa ziyarar ta’aziyya ko kuma dogaro da hare-haren sojoji waɗanda ke gajiyar da jami’an tsaro.
"Ya fi kyau gwamna ya kashe kuɗinsa wajen ceton rayuka fiye da kashe biliyoyi wajen ta’aziyya. Rayuwar mutum ɗaya ta fi muhimmanci kan abubuwan siyasa."

Kara karanta wannan
Bayan tsawon lokaci, gwamna ya tabbatar da fara tattaunawar sulhu da 'yan bindiga
- Mallam Abubakar Yusuf
Yayin mayar da martani ga masu adawa da tattaunawa da ‘yan bindiga, Mallam Abubakar ya jaddada cewa tattaunawa ta tabbatar da ingancinta a wasu wuraren da ake samun rikici a duniya, rahoton Tribune ya tabbatar da labarin.
"Ko manyan kasashe sun taɓa shiga tattaunawa da kungiyoyi irin su Taliban, Al-Qaeda, da Houthis. Tattaunawa ba rauni ba ce; magana ce ta ceton rayuka."
- Mallam Abubakar Yusuf

Source: Twitter
An soki wasu gwamnonin jihohin Arewa
Dattijon ya kuma soki gwamnonin da ke cewa suna sane da motsin ‘yan bindiga amma ba sa bayar da bayanan sirri ga hukumomin tsaro.
“Bai dace ba shugaba ya ce ya san inda ‘yan ta’adda suke amma ya kasa mika wannan bayani ga jami’an tsaro. Irin wannan magana ta siyasa rashin gaskiya ce."
- Mallam Abubakar Yusuf
Kungiyar NEPG ta kuma kare ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro da sauran mambobin kwamitin da ke jagorantar shirin zaman lafiya, tana gargadin cewa kada a sanya siyasa ko raina kokarin da suke yi.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar yin raga-raga da 'yan ta'adda a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun kashe 'yan ta'adda fiye da 20 bayan sun kai farmaki a maboyarsu da ke karamar hukumar Kankara.
Hakazalika, jami'an tsaron sun samu nasarar kubutar da mutanen da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

