'Dole ka Zo,' ’Yan Sanda na Shirin Daukar Mataki kan El Rufai bayan kin Amsa Gayyata

'Dole ka Zo,' ’Yan Sanda na Shirin Daukar Mataki kan El Rufai bayan kin Amsa Gayyata

  • ’Yan sanda sun bukaci tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da wasu manyan jam’iyyar ADC su bayyana da kansu gabansu
  • Ana tuhumar su da laifuffukan haɗin baki, tayar da tarzoma, barna da kuma jikkata mutane bayan wani taro da suka yi a Kaduna
  • A karon farko da aka gayyace su, El-Rufai da sauran sun tura lauyoyi a matsayin wakilai, amma rundunar ta ce dole su zo da kansu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Rundunar ’yan sanda ta jihar Kaduna ta dage cewa dole tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, da wasu shugabanni shida na jam’iyyar ADC su bayyana a gabanta.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar na bukatar su bayyana da kansu a gaban sashen binciken manyan laifuffuka (CID) domin amsa gayyata.

Kara karanta wannan

Ambaliya ta kashe rayuka a Zariya, ruwa ya tafi da wasu mutane

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da kwamishinan 'yan sandan Kaduna, CP Rabiu Muhammad.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da kwamishinan 'yan sandan Kaduna, CP Rabiu Muhammad. Hoto: @elrufai, @kadunapoliceHQ
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa kakakin rundunar, Mansir Hassan, ya ce rundunar ba za ta amince da wakilai ba, domin umarnin ya shafi mutanen da aka gayyata kai tsaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ta ce duk da cewa wadanda aka gayyata sun tura lauyoyi da shugabannin jam’iyyarsu a matsayin wakilai, ba zai maye gurbin bayyana da kansu ba.

Dalilan gayyatar El-Rufai da sauran 'yan ADC

Tun farko, rundunar ’yan sanda ta gayyaci El-Rufai da shugabannin jam’iyyar ADC domin amsa tambayoyi kan zargin aikata laifuffuka.

Ana zarginsu da laifuffuka da suka hada da haɗin baki wajen aikata laifi, tayar da tarzoma, aikata barna, da kuma haddasa rauni ga mutane.

Punch ta wallafa cewa a lokacin da suka samu gayyatar, sun kasa zuwa da kansu, amma sun tura wakilai daga cikin lauyoyi da kuma shugabannin jam’iyyar domin wakiltarsu.

Wannan mataki da su El-Rufa'i suka dauka ne ya sanya rundunar 'yan sanda cewa ba ta amince da shi ba.

Kara karanta wannan

Harin Kaduna: El Rufa'i, jagororin ADC sun yi fatali da gayyatar ƴan sanda

'Yan sanda sun bukaci ganin El-Rufa'i

Da yake jawabi, kakakin rundunar ya tabbatar da cewa suna bukatar ganin wadanda aka gayyata ne kai tsaye.

Ya bayyana cewa:

“Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da sauran wadanda aka gayyata ba su zo da kansu ba.
"Sun tura lauyoyi da shugaban jam’iyyarsu a matsayin wakilai. Mun shaida musu cewa ba haka muka ce ba, dole su bayyana da kansu.”
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IG Kayode
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IG Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Hassan ya kara da cewa rundunar na jiran su su zo don amsa tambayoyin da aka shirya musu, kafin a yanke hukunci kan matakin da za a dauka a gaba.

Ya kara da cewa:

“Har yanzu muna jiran su su girmama wannan gayyata. Idan sun ki, za mu bayyana matakin da za mu dauka,”

Bisa tsarin doka, wanda aka gayyata zuwa gaban ’yan sanda idan ya gaza bayyana, rundunar na da ikon ɗaukar matakan tilastawa, ciki har da kama shi domin tabbatar da bin doka.

Malam El-Rufa'i ya yi karar 'yan sanda

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya kai karar rundunar 'yan sandan jihar.

Tsohon gwamnan ya shigar da kwamishinan 'yan sanda da wasu jami'ansa wajen hukumar 'yan sanda ta kasa bayan an gayyace shi.

El-Rufa'i ya shigar da korafi ne saboda zargin da ya ke na cewa ba a masa adalci ba bayan wani hari da aka kai musu suna taro kuma aka gayyace shi ya amsa tambayoyi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng