'Yan Sanda Za Su Cire Aljihu a Kayan Jami'ansu domin Daƙile Cin Hanci? An Gano Gaskiya

'Yan Sanda Za Su Cire Aljihu a Kayan Jami'ansu domin Daƙile Cin Hanci? An Gano Gaskiya

  • Wasu shafukan yanar gizo sun yi ta yada ikirarin cewa gwamnatin kasar nan za ta cire aljihu daga kayan ‘yan sanda
  • Rundunar yan sanda dai a Najeriya tana yawan shan suka kan zargin karbar cin hanci daga yan Najeriya wanda ake yawan tuhumarsu
  • Haka kuma hoton da aka yi amfani da shi daga bikin kaddamar da sababbin kayan SPY Police a shekarar 2024 ne, ba batun aljihu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An yi yada jita-jitar cewa akwai wani sabon mataki da rundunar yan sanda za su dauka kan yaki da cin hanci.

Wasu shafukan yanar gizo sun yada cewa gwamnatin tarayya na shirin cire aljihu daga kayan ‘yan sanda don hana cin hanci.

An ƙaryata shirin cire aljihun a rigar yan sanda saboda cin hanci
Babban Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun da rigar jami'an 'Spy Police' a Najeriya. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Sauya kayan 'yan sanda: Karairayi da aka yadawa jama'a

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan bindigan da suka kai hari masallaci ana sallar asuba

A wani bincike da TheCable ta yi, ta gano gaskiya kan rade-radin da ake yadawa game da lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ikirari ya bayyana hoton wani jami’in ‘yan sanda dauke da kayan 'SPY Police', da rubutun Turanci kan cewa za a cire aljihu a kayan yan sanda.

Wani mai amfani da X mai suna @ekwulu ya wallafa hoton inda ya yi tambaya da cewa:

"Waye yake yi wa wadandan mutane tunani?"

Wasu daga cikin masu amfani da shafin sun yi tsokaci cikin barkwanci, suna cewa idan an cire aljihu, za su fara amfani da na'urar cire kudi ta 'POS' wajen karɓar cin hanci.

Yadda jita-jitar ta yi tasiri a kafofin sadarwa

Haka kuma wani shafin Facebook mai suna “News in Naija” ya wallafa wannan ikirari inda wasu suka yi sharhi cewa ‘yan sanda za su fara ɓoye kuɗi a takalmi ko riguna.

Majiyoyinmu ta lura cewa wannan labari ba ya cikin manyan jaridun ƙasa ko shafukan gwamnati, sai dai a kananan kafofin sadarwa da shafukan sada zumunta kawai.

Kara karanta wannan

'Abubuwa 4 ne ke rura wutar ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya nemo mafita ga Arewa

Bincike ya nuna cewa ikirarin ya fito tun a wani shafi a shekarar 2017, abin da ke nuna cewa tsohon labari ne aka dawo da shi.

An tsage gaskiya kan cewa yan sanda za su cire aljihun kayansu saboda hana cin hanci
Babban Sufeta-janar na yan sanda a Najeriya. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

A ina aka samo hoton da ake yadawa?

Idan har lamarin bai tabbata, mutane za su so jin inda aka samo hoton kayan jami'an.

Hoton da aka yi amfani da shi na DIG Bala Ciroma ne, wanda ya wakilci IGP Kayode Egbetokun wajen kaddamar da sababbin kayan 'SPY Police' a watan Satumba 2024.

'SPY Police', a cewar dokar rundunar ta 2020, su ne jami’an da ake ɗauka na wucin gadi, yawanci don kare gine-ginen gwamnati ko na masu zaman kansu.

Wadannan jami’ai ba su karɓar albashi daga rundunar kai tsaye, sai dai daga hukumomin gwamnati ko kamfanoni da suka nema a ba su irin wannan tsaro.

'Yan sanda suna bincike bayan tsintar gawa

Mun ba ku labarin cewa rundunar yan sanda ta fara bincike bayan tsintar gawa a kusa da majalisar wakilai a Abuja.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka

Adeh ta ce an ajiye gawar a asibitin Asokoro, yayin da ake ci gaba da kokarin gano abin da ya haifar da mutuwar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.