Kaduna: Bayan Kwanaki a Hannun 'Yan Ta'adda, Kansila Ya Shaki Iskar Yanci

Kaduna: Bayan Kwanaki a Hannun 'Yan Ta'adda, Kansila Ya Shaki Iskar Yanci

  • Kansilan Gwantu da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna ya samu kubuta daga hannun 'yan ta'adda da su ka dauke shi
  • Kwanaki hudu da suka wuce wasu 'yan ta'adda suka fada cikin gidansa da daddare, sannan su ka yi awon gaba da shi iyalansa na kallo
  • Shugaban karamar hukumar Sanga, Anto Usman ya tabbatar da cewa Kansilan ya dawo gida, yayin da rahotanni su ka ce da da aka biya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna David Ali, Kansilar mazabar Gwantu a karamar hukumar Sanga, jihar Kaduna, ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane.

David Ali ya shaki iskar 'yanci ne bayan kwana huɗu da sace shi a gidansa da ke cikin garin Gwantu a wani hari da aka kai yankin.

Kara karanta wannan

Mamakon ruwa ya 'daidaita jama'a a Kaduna, sama da mutum 500 sun rasa matsuguni

An sako Kansila a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna inda aka yi awon gaba da kansila Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa an sace David da 12.00 na dare a ranar Alhamis da ta gabata, lokacin da ’yan bindiga guda biyar da suka kai farmaki gidansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce miyagun mutanen sun kutsa cikin gidansa tare da dauke shi iyalansa na kallo, lamarin da ya tayar da hankali a cikin al’umma.

'Yan ta'adda sun sako Kansila a Kaduna

Daily Post ta wallafa cewa Shugaban karamar hukumar Sanga, Anto Usman, ya tabbatar da sakin Ali a ranar Talata.

Da ya ke bayar da tabbacin, Shugaban ya ce an sako Kansilan ne a tsakanin 8.00 zuwa 9.00 na dare a ranar Litinin.

Rahonni sun bayyana cewa iyalin David Ali sun biya N4,000,000 kafin a sako shi bayan shafe tsawon kwanaki a tsare.

Ana hasashen har yanzu akwai matsalar tsaro a Kaduna
Hoton gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda tsaro, ya shaida cewa an sako Ali ne a dajin da ke kusa da Ninzo, bayan da iyalansa suka biya kudin fansa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi dirar mikiya a kan mazauna Zamfara, sun kashe mutane

Majiyar ta ce:

“An sake shi ne saboda addu'o'in al'umma. Muna godiya ga Allah da ya tsare rayuwarsa."

Akwai matsalar tsaro a jihar Kaduna

Shugaban karamar hukumar, Anto Usman ya bayyana cewa duk da an samu saukin ta'addanci a yankin, har yanzu ana fuskantar ƙalubale saboda masu bayar da bayanai ga ’yan ta’adda.

Ya ce:

“Muna ci gaba da gudanar da taro a kan tsaro lokaci-lokaci, kuma a bana mun kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a garkuwa da mutane, kuma yanzu haka suna fuskantar shari’a."

Ya kuma yabawa Gwamna Uba Sani saboda ƙoƙarinsa na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro a fadin jihar, yana mai cewa hakan yana rage tashin hankali.

Har ila yau, al’umma da magoya baya sun bayyana farin cikinsu a kafafen sada zumunta, suna bayyana Ali a matsayin wakilin gaskiya da ya fuskanci mawuyacin hali.

An sace shugaban karamar hukuma

A baya, mun wallafa cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban riko na ƙaramar hukumar Ukum a jihar Binuwai, Haanongon Gideon, tare da wasu mutane guda uku.

Kara karanta wannan

Wasu ma'aikata sun jawo wa kansu, gwamna ya kore su daga aiki nan take

'Yan ta'adda sun yi garkuwa da su ne da sanyin safiya a hanyarsu zuwa jana’izar Sarkin ƙaramar hukumar Katsina‑Ala, Ter Katsina‑Ala, Fezanga Wombo da ya rifa mu gidan gaskiya.

Kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da yawon buɗe ido na jihar Benue, Matthew Abo, ya tabbatar da sace shugaban ƙaramar hukumar, amma ya ce bai ga jana'izar ba aka dauke su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng