Taron Maulidin Annabi SAW Ya Hargitse, An Kama Mutane 30 Dauke da Makamai

Taron Maulidin Annabi SAW Ya Hargitse, An Kama Mutane 30 Dauke da Makamai

  • Yan sanda sun cafke mutane 30 da ake zargi da aikata laifuffukan da suka shafi ta'addanci da daba a jihar Neja
  • An kama wadannan mutanen ne a wuraren da musulmi suka taru suna bikin Maulidin Annabi Muhammad SAW a birnin Minna
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Neja ya ce yanzu haka ana kan bincike, ya kuma bayyana makaman da aka kwato

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Minna, jihar Niger - Wasu da ake zargin miyagun 'yan daba ne sun shiga hannu a wurin tarurrukan Maulidi a Minna, babban birnin jihar Neja.

Dakarun yan sanda sun damke matasa akalla 30 da ake zargi da hannu a ayyukan 'yan daba da ta'addanci a bukukuwan maulidin da aka gudanar ranar Asabar, 6 ga watan Satumba, 2025 a Minna.

Jihar Neja.
Taswirar jihar Neja inda aka samu makamai wajen Maulidi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja ce ta bayyana hakan, ta ce an kama wadanda ake zargin ne a wani samame da jami'ai suka kai, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan bindigan da suka kai hari masallaci ana sallar asuba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama mutane 30 a Minna

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da samun wannan nasara a sanarwar da ya fitar a Minna.

Ya ce an cafke mutanen ne a wani samame na musamman da aka kaddamar domin dakile ayyukan ta’addanci da sauran miyagun dabi’u.

A rahoton Punch, Wasiu Abiodun ya ce:

“A ci gaba da yaki da ta'addanci da sauran miyagun laifuffuka a Jihar Neja, ranar 6 ga Satumba, 2025, daga karfe 7:00 na safe zuwa 9:00 na dare, ’yan sanda da ke sintiri sun kama mutum 30 a wurare daban-daban yayin gudanar da Mauludi a Minna.

Wuraren Maulidin da aka kama miyagu

Ya ce wuraren da aka cafke wadanda ake zargin sun hada da Angwan-Sarki, Limawa, Angwan-Daji, New-Market, Sabon-Gari, titin Kuta, Obasanjo Complex, titin Ogbomosho, titin Lagos da Central Roundabout.

Kakakin yan sanda ya lissafo abubuwan da aka kwato ciki har da wukake guda uku, gatari uku, sandar ƙarfe guda daya, almakashi, tabar wiwi, kayan shan shisha da wasu sinadarai da ake amfani da su wajen aikata miyagun ayyuka.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Katsina, an tura miyagu zuwa barzahu

Abiodun ya bayyana cewa dukkan wadanda aka kama suna karkashin bincike a halin yanzu, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu kan laifuffuka daban-daban.

Sufetan yan sandan Najeriya.
Hoton sufetan yan sandan Najeriya, IGP Kayode a wurin taro Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda sun jaddada kudirin samar da tsaro

Rundunar ta jaddada kudirinta na ci gaba da gudanar da sintiri da tsaurara matakai domin tabbatar da zaman lafiya musamman a lokutan bukukuwa da tarukan jama’a.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahoto kan duk wata motsi ko shakku da ka iya haifar da barazana ga tsaro domin baiwa jami’an tsaro damar daukar matakin gaggawa.

'Yan sanda za su ba da tsaro a Maulidin 2025

A wani labarin, kun ji cewa rundunar yan sanda ta sha alwashin daukar matakan da suka dace domin tabbatar da an yi tarukan maulidi cikin kwanciyar hankali a Jigawa.

Kakakin yan sandan Jigawa, SP Shi’isu Adam, ya bayyana cewa rundunar ta dauki tsauraran matakai don tabbatar da tsaro yayin bikin Mauludi.

Ya jaddada kudirin rundunar wajen gudanar da aikin tsaro bisa adalci, kwarewa da kuma hada kai da kowace kungiya a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262