Mamakon Ruwa Ya 'Daidaita Jama'a a Kaduna, Sama da Mutum 500 Sun Rasa Matsuguni
- Ruwan sam kamar da bakin kwarya ya raba iyalai sama da 540 da gidajensu yayin da ake kara hasashen ruwa mai karfi a wasu jihohi
- Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar ta ce akala gidaje 171 sun lalace sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka samu na tsawon kwana biyu
- KADSEMA ta ce tana aiki da hukumomin bada agaji don samar da mafita da rage hadurra nan gaba yayin da aka dauki matakin gaggawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kaduna (KADSEMA) ta bayyana cewa mamakon ruwa a jihar ya raba jama'a da dama da muhallansu.
A cewar KADSEMA, sama da iyalai 545 ne ambaliya ta shafa, yayin da gidaje 171 suka lalace sakamakon ruwan sama mai karfi da aka tafka a ranar 4 zuwa 5 ga watan Satumba, 2025.

Source: Original
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar, Usman Mazadu ne ya bayyana halin da ake ciki a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ambaliya: Ana aikin ceto a jihar Kaduna
Daily Post ta wallafa cewa Usman Mazadu ya ce ana gudanar da aikin hadin gwiwa domin tantance barnar da ambaliyar ta kafin daukar matakin gaggawa.
A cewarsa, ruwan sama ya haddasa ambaliya mai ƙarfi da ta tilasta jami’ansu gaggawar kwashe mutane daga wasu yankuna da ruwa ya mamaye.
Ya bayyana cewa ambaliyar ta fi kamari a unguwar Kigo, inda gidaje 69 da iyalai 276 suka tsinci kansu cikin ruwa tsulum.
Ya kara da cewa haka kuma wata makarantar firamare mai zaman kanta, Merits Kids Academic School, tana daga cikin wuraren da ruwa ya mamaye baki daya.
Sauran unguwannin Kaduna da ke cikin matsala
Shugaban KADSEMA ya kuma lissafa wasu yankunan da bala’in ya shafa, kamar su: Rifin Guza, inda ruwan da ya mamaye gidan jama'a daTudun Wada da Ungwan Rimi.
Ya kara da cewa a Malali G.R.A, wata gada da ke haɗa unguwar da titin Libreville ta rushe gaba ɗayanta, da ma sauran unguwanni a jihar.

Source: Original
Ya ce ana gudanar da rijistar dukkannin iyalan da bala’in ya rutsa da su, domin tabbatar da cewa agaji ya isa ga waɗanda suka fi buƙata.
Ya ce gwamnati za ta samar da mafaka ta wucin gadi, abinci da agajin lafiya ga waɗanda suka rasa matsuguni.
Usman Mazadu ya tabbatar da cewa suna aiki kafada da kafada da hukumomin haɗin guiwa kamar NEMA, NSCDC, Christian Aid, Red Cross da hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna domin ceto rayuka da dukiyoyi.
Ya ce:
“Bayan matakan gaggawa, muna tsara shirin taimaka wa al’ummomin da abin ya shafa su sake gina rayuwarsu da rage haɗurran amfkuwar ambaliya a nan gaba.”
An yi hasashen sheka ruwa a wasu jihohi
A baya, mun wallafa cewa Hukumar NiMet, ta bayyana cewa za a sami ruwan sama mai yawa a sassan Arewa da wasu jihohin Arewa ta Tsakiya a ranar Talata, 9 ga Satumba, 2025.
Hukumar hasashen yanayi ta kasa, ta yi gargadin cewa mamakon ruwan ka iya jawo ambaliya da sauran haɗurran da ke tattare da ruwan sama mai haɗe da iska da tsawa.
Hukumar ta ce mamakon ruwan da za a yini ana zuba shi na iya janyo tsaiko ga zirga-zirga, musamman a manyan tituna, yayin da iska da ruwa mai ƙarfi za su iya haddasa haddura.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


