Babbar Magana: Lauyan Sowore Ya Nemi Su Hadu a Kotu da Tinubu
- Lauya ya soki bukatar DSS ta rufe shafin Facebook Omoyele Sowore, yana mai cewa hakan ya saba wa doka
- Ya ce wannan mataki na iya zama barazana ga ‘yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulki ya tanada
- Lauyan ya roki Meta da kada ya amince da bukatar DSS domin kauce wa kafa mummunan tarihi a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Lauyan dan gwagwarmaya kuma mai fafutuka, Omoyele Sowore, ya yi rubutu zuwa ga kamfanin Meta da ya mallaki Facebook, yana kalubalantar bukatar hukumar tsaro ta DSS.
Hakan na zuwa ne bayan hukumar DSS ta bukaci kamfanin Meta ya rufe shafin Facebook din Sowore kan rubutun da ya yi a kan Bola Tinubu.

Source: Twitter
A wasikar da ya wallafa a Facebook, lauyan ya ce bukatar ba ta da tushe a tsarin doka, kuma idan aka amince da ita, za ta yi mummunan tasiri kan dimokuradiyyar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, lauyan ya ce wannan yunƙuri wani salo ne na siyasa wanda ba ya cikin aikin da ya kamata hukumar tsaro ta yi wa kasa.
Me ya hada Sowore da DSS a Najeriya?
Hukumar DSS ta yi rubutu zuwa ga Meta tana neman a rufe shafin Facebook na Omoyele Sowore bisa dalilin wani rubutu da ya wallafa.
Sai dai lauyoyinsa, karkashin jagorancin Inibehe Effiong, sun ce rubutun bai karya ka’idojin Meta ba, kuma babu wani dalili na doka da ya halatta wannan bukata.
Sun kuma zargi DSS da amfani da ikon gwamnati wajen kare mutuncin shugaba Tinubu ta hanyar tozarta kundin tsarin mulki.
An bukaci Tinubu ya kai Sowore kotu
A cikin rubutunsu, lauyoyin sun bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai kai karar Sowore kotu ba, don haka babu hujja ga DSS ta tsoma baki.
Sun ce idan Shugaba Tinubu yana ganin an ci mutuncinsa, ya kamata ya je kotu domin kare kansa, maimakon dogara da DSS.

Kara karanta wannan
Lokaci ya yi: Yanayin da wani likita ya rasu a asibiti ya ja hankali, NARD ta yi magana
Haka kuma, sun ce wannan yunƙuri ne na nuna son rai da kuma yunƙurin murkushe muryar 'yan gwagwarmaya a Najeriya.
Kiran Sowore ga kamfanin Meta
Rahoton Arise News ya nuna cewa lauyoyin sun yi kira ga Meta da kada ta amince da wannan bukata da suka ce bata bisa doka kuma tana cike da danniya
Sun yi gargadin cewa idan Meta ta amince da bukatar DSS, hakan zai kafa tarihi mummuna wanda zai karfafa gwamnati wajen yakar muradun ‘yan adawa.

Source: Facebook
Sun roki Meta ta tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin fadin albarkacin baki da ya kamata ya kasance ginshikin kafar sadarwar zamani.
A yanzu haka dai kallo ya koma kan kamfanin Meta domin ganin matakin da zai dauka game da takaddamar.
Sowore ya ce 'yan sanda sun karya shi
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Omoyele Sowore ya yi ikirarin an karya shi a kwanakin baya.
Ya yi maganar ne bayan an rufe shi bayan amsa gayyatar 'yan sanda a birnin tarayya Abuja kan wasu zarge zarge.
Magoya bayan dan gwagwarmayar sun gudanar da zanga zanga a hedkwatar 'yan sanda da ke Abuja bayan tsare shi da aka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
