Wata Sabuwa: Bayan Cika Wata 6, Majalisa ta Hana Natasha Komawa Aiki
- Majalisar dattawa ta ki amincewa da bukatar Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma bakin aiki bayan wa’adin dakatarwarta na wata shida
- Rahoto ya ce majalisar ta ce dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Maris, 2025, kuma har yanzu shari’a na ci gaba a kotun daukaka kara
- Majalisar ta bayyana cewa ba za a ɗauki wani mataki ba kan Natasha ba sai kotu ta yanke hukunci sannan za ta yi bitar dakatarwar da aka mata
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Majalisar dattawa ta ce Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ba ta da ikon komawa majalisa a yanzu.
Sanata Natasha na shirin komawa majalisa ne bayan dakatarwar da aka yi mata na tsawon wata shida a baya.

Kara karanta wannan
An tsinci gawa gefen ofishin sakataren gwamnatin Tinubu, majalisa ta yi karin haske

Source: Facebook
Leadership ta wallafa cewa matakin ya biyo bayan wata wasika da mukaddashin sakataren majalisar, Dr. Yahaya Danzaria, ya aikawa Sanatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpoti-Uduaghan ta nemi komawa zauren majalisar ranar 4 ga Satumba, 2025, tana mai cewa wa’adin dakatarwar ya kare, amma majalisar ta ce ba zai yiwu ba.
Asalin rikicin Natasha da majalisar dattawa
Tun a ranar 6 ga Maris, 2025, majalisar dattawa ta dakatar da Natasha Akpoti saboda zargin rashin da’a, bayan rikicinta da shugaban majalisar, Godswill Akpabio kan wajen zama.
Bayan dakatarwar, an garzaya da batun kotu, inda babbar kotun tarayya ta Abuja ta yanke hukuncin goyon bayan majalisar.
Sai dai Natasha ba ta gamsu ba, ta kuma daukaka kara zuwa kotun daukaka kara domin neman adalci.
Tun daga lokacin, ta ci gaba da ikirarin cewa wa’adin dakatarwar ya kare, tana bukatar ta koma bakin aiki a majalisa.
Majalisa ta hana Sanata Natasha komawa aiki
A wasikar da Dr. Danzaria ya sa wa hannu ranar 4 ga Satumba, 2025, majalisar ta bayyana cewa ba za a bar Sanatar ta koma aiki ba saboda dakatarwar ba ta kare ba.
Tribune ta rahoto cewa wasikar ta kara da cewa:
“Lamarin yana gaban kotu, kuma har sai an kammala shari’a sannan majalisar ta yi bitar matakin dakatarwar, babu wani matakin da za a iya dauka na dawo da ke bakin aiki.”
Majalisar ta kuma tabbatar mata cewa za a sanar da ita matakin karshe bayan kotun daukaka kara ta yanke hukunci.

Source: Facebook
Sanata Natasha da fafutukar da ta yi
Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi kaurin suna wajen yin adawa da wasu tsare-tsaren da ke cikin majalisar dattawa, inda a lokuta da dama take ikirarin cewa ana tauye mata ‘yanci.
Tuni ta sha alwashin ci gaba da fafutukar ganin kotu ta ba ta damar komawa majalisa, tana mai cewa dakatarwar ba ta da tushe a doka.
Obasanjo ya caccaki 'yan majalisa
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi wa 'yan majalisar Najeriya kaca-kaca.
Obasanjo ya yi magana ne kan makudan kudin da 'yan majalisar ke samu da sunan gudanar da ayyuka a mazabunsu.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa kudin da 'yan majalisar ke karba domin ayyukan tamkar fashi ne rana tsaka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

