Hausawa Sun kai Kuka wajen Kwankwaso bayan Shiga Matsala a Kasuwar Benue

Hausawa Sun kai Kuka wajen Kwankwaso bayan Shiga Matsala a Kasuwar Benue

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da wata tawaga ta ‘yan Arewa masu kasuwancin lemo a Jihar Benue a Nasarawa
  • ‘Yan kasuwar sun koka da matsalolin da ke hana harkarsu tafiya yadda ya kamata, suna cikin yajin aiki a halin yanzu
  • Kwankwaso ya ce zai tattauna da Gwamnan Jihar Benue domin a nemo hanyar magance matsalolin da suke fuskanta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa – Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi bakuncin wata tawaga ta ‘yan Arewa masu harkar kasuwancin lemo a jihar Benue.

Sanata Kwankwaso ya gana da su ne a wani taro da aka gudanar ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025 a jihar Nasarawa.

Kwankwaso yayin ganawa da masu sayar da lemo a Benue
Rabiu Kwankwaso yayin ganawa da masu sayar da lemo a Benue. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Sanata Kwankwaso ya yi ne a cikin wani sako da hadiminsa, Saifullahi Hassan ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

'Abubuwa 4 ne ke rura wutar ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya nemo mafita ga Arewa

Kukan da masu lemon Benue suka yi

Tawagar ta shaida wa Kwankwaso cewa harkarsu ta durƙushe saboda matsaloli da dama da suke fuskanta a fannin kasuwanci da sufuri.

Sun bayyana cewa saboda tsananin matsalar da ake ciki, a yanzu haka suna cikin yajin aiki domin nuna rashin jin daɗinsu da kuma neman a ji ƙorafinsu.

Alkawarin da Kwankwaso ya yi musu

Da yake maida martani, Kwankwaso ya tabbatar musu cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen kawo sauƙi a harkokinsu.

Ya ce zai tattauna da gwamnan jihar Benue domin a nemo mafita mai dorewa, wacce za ta ba su damar ci gaba da sana’arsu ba tare da cikas ba.

Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Yadda ake noman lemo a jihar Benue

Wani rahoto na jaridar Daily Trust ya nuna cewa jihar Benue tana da amfanin gona fiye da guda 120 da ake nomawa.

Wannan ya haɗa da doya, gero, wake, masara, dankali, waken suya da kuma kayan marmari irin su lemo da mangwaro.

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

Benue na alfahari da kasancewarta babbar cibiyar lemo a Najeriya, musamman a karamar hukumar Ushongo, da kuma Konshisha, Gboko da Vandeikya da ke biye da ita.

A yawancin gidaje a waɗannan yankuna, ana iya samun gonakin lemo, ko da kuwa masu gonakin suna zaune a wasu jihohi daban.

Yadda ake kasuwancin lemo a Benue

Masu sayen lemo daga jihohi daban-daban kamar Borno, Kano, Imo, Ogun da Legas kan zo da manyan motoci domin ɗaukar kaya a Benue

Yawancin mutanen Vandeikya suna da gonakin lemo kuma suna da matasa da ke shiga tsakani wajen sayar da lemu ga ‘yan kasuwa daga Arewa da Kudu maso Gabas.

Hakan ya tabbatar da irin tasirin da noman lemo ke da shi wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da aikin yi ga dubban mutane a jihar Benue da ma Najeriya baki ɗaya.

Kwankwaso ya gana da Hausawa a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da Hausawa da aka rusa wa kasuwa a jihar Legas.

'Yan kasuwar sun koka da cewa sun shafe shekaru suna gudanar da kasuwanci a wajen kuma aka rusa musu shaguna dare daya.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi alkawarin shiga tsakani domin ganin an daidaita tsakaninsu da gwamnatin jihar Legas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng