An Tsinci Gawa Gefen Ofishin Sakataren Gwamnatin Tinubu, Majalisa Ta Yi Karin Haske

An Tsinci Gawa Gefen Ofishin Sakataren Gwamnatin Tinubu, Majalisa Ta Yi Karin Haske

  • Majalisar Wakilan Tarayya ta yi karin haske bayan samun gawar wani a gefen majalisar a ranar Lahadi a Abuja
  • Majalisar ta bayyana cewa an gano gawar da ba a san na waye ba a cikin wata mota kusa da ofishin sakataren gwamnati
  • Kakakin Majalisar, Akin Rotimi ya ce rahoton 'yan sanda ya nuna mutumin ma'aikaci ne wanda tuni aka dauki mataki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Majalisar Wakilai ta fito da bayanai bayan tsintar gawar wani mutum kusa da majalisar domin cire shakku ga al'umma.

Majalisar wakilan tarayyar ta bayyana rahoton gano gawar wani da ba a sani ba a kusa da Majalisar a ranar Lahadi a Abuja.

Majalisa ta fadi yadda aka samu gawa kusa da ita a Abuja
Shugaban majalisar dokokin Najeriya, Hon. Tajudden Abbas. Hoto: House of Rpresentatives.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar a shafinta na X a jiya Litinin 8 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke bayan tono gawar malamin Musulunci a kabari aka kona ta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun shiga lamarin a Abuja

Hakan ya biyo bayan tsintar gawar mutumin da ya tayar da hankulan mutane musamman da ke kusa da wurin.

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun rundunar yan sanda, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Adeh ta ce an ajiye gawar a Asibitin Janar na Asokoro, yayin da ake ci gaba da kokarin gano abin da ya haifar da mutuwar.

Ta bayyana cewa rundunar ta samu kiran gaggawa game da lamarin, inda nan take ta tura jami’anta zuwa wurin da abin ya faru.

Samun gawa kusa da majalisa ya firgita al'umma a Abuja
Tsohon ginin majalisar tarayya kafin yi masa kwaskwarima da ke Abuja. Hoto: The Nigeria Senate.
Source: Twitter

Majalisar wakilai ta yi karin haske kan lamarin

Kakakin majalisar, Hon. Akin Rotimi Jr shi ya bayyana hakan yana dogaro da rahoton hukumomin 'yan sanda kan lamarin.

Ya ce shugabancin Majalisar na da nauyin sanar da jama’a daidai don kauce wa jita-jita da yada labaran da ba su da tushe.

Rotimi ya nakalto DPO na ofishin yan sanda na Majalisar cewa ana zaton mamacin ma’aikaci ne a wurin gine-gine, an same shi da safe a mota kirar Peugeot.

Kara karanta wannan

An samu aukuwar mummunar ambaliya a Taraba, kauyuka 7 sun nutse a cikin ruwa

Motar mai lambar rijista BWR-577 BF ta kasance a wajen kofar ginin, kusa da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

Sanarwar ta ce:

“An gano gawar mutumin a jingine a cikin motar matacce a bayan kujerar mota, kuma babu alamun wani abu, an kai gawar asibiti domin bincike."

Alkawarin majalisa ga al'umma kan lamarin

Ya ce Majalisar tana aiki tare da hukumomin tsaro da agaji domin tabbatar da cikakken bincike kan wannan al’amari.

Rotimi ya yaba da gaggawar martanin ’yan sanda, inda ya ce Majalisar za ta ci gaba da sa ido yayin da ake binciken.

“A madadin Majalisar Wakilai, muna jajanta wa iyali da abokan mamacin, za mu sanar da jama’a yadda ake yin bincike."

- Hon. Akin Rotimi Jr

An tsinci gawar budurwa kusa da masallaci

A baya, mun ba ku labarin cewa rundunar ƴan sanda ta gano gawar wata budurwa mai suna Halimat a kusa da wani masallaci a jihar Osun.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sanda ya ce sun samu alamu biyu a wurin, sun ji warin fiya-fiya kuma sun tsinci takarda.

Ya ce suna kan gudanar da bincike kuma sun samu ganin ɗaya daga cikin ƴan uwanta, wanda ya fara ba su cikakkun bayanai game da haka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.