Kwana Ya Kare: Bako daga Kasar Waje Ya Yi Mutuwar da ba a Yi Tsammani ba a Abuja

Kwana Ya Kare: Bako daga Kasar Waje Ya Yi Mutuwar da ba a Yi Tsammani ba a Abuja

  • An shiga tashin hankali a wani otal da ke Abuja yayin da bako daga kasar Masar, Mohammed Saleh ya fadi ya mutu ba zato da tsammani
  • An ruwaito cewa marigayin ya fadi kasa ne kwatsam yana tsakiyar cin abinci da abokansa a daren ranar Juma'ar da ta wuce
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da fara bincike don gano abin da ya haddasa mutuwar dan kasar wajen

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wani ɗan asalin ƙasar Masar mai suna Mohammed Saleh ya rasu bayan da ya fāɗi a ɗaya daga cikin otal-otal da ke unguwar Wuse Zone 4, Babban Birnin Tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya gamu da ajali ne a lokacin da yake cin abincin dare tare da wasu mutane a otal din a ranar Juma'a da ta gabata.

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

Birnin tarayya Abuja.
Hoton taswirar babban birnin tarayya Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ne ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na X ranar Lahadi, 7 ga watan Satumba, 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda bako daga Masar ya rasu a otal a Abuja

A cewar shi, lamarin ya faru ne da daren Juma’a lokacin da Mohammed Saleh, mai shekaru 56, yake cin abinci tare da wasu mutane uku a Abuja Intercontinental Hotel.

Rahoton ya ƙara da cewa shugaban jami'an tsaron otal ɗin, Francis Yusuf, ne ya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda na Wuse da ke cikin Abuja.

Majiyoyi sun shaida wa majiyar cewa farat daya suka ga marigayin, Mohammed Saleh, ya yanke jiki ya fāɗi lokacin da yake cin abinci da abokan zamansa a otal ɗin.

"Mun yi hanzarin kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda da misalin ƙarfe 9:24 na dare,” in ji sanarwar.

Wane mataki jami'an 'yan sanda suka dauka?

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

Bayan faruwar haka, an garzaya da Saleh zuwa asibitin King’s Care Hospital da ke Wuse Zone 4, kafin daga bisani a mayar da shi Wuse District Hospital, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

A halin yanzu, an kai gawar mamacin dakin ajiyar gawarwaki domin gudanar da bincike kafin birne shi.

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta fara bincike don gano dalilan da suka haddasa mutuwar.

Wannan ba shi ne karon farko da aka samu rahoton rasuwar baƙi a otal-otal a Najeriya ba.

A baya an yi irin wannan a Legas, inda aka samu mutuwar wani ɗan ƙasar Kolombiya mai shekaru 80, Quesada Alfonso, a wani otal da ke FESTAC Town, Legas.

Dalarun yan sanda.
Hoton jami'an rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: Nigeria Police Force
Source: Getty Images

Rundunar 'yan sanda ta shirya fitar da sanarwa

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sanda a Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da cewa sun samu rahoto mutuwar Mohammed amma ta ce za ta fitar da cikakken bayani daga baya.

Rahotanni sun nuna cewa yawanci irin waɗannan mutuwar kan kasance sakamakon rashin lafiya ko kuma wasu cututtukan da ba a sani ba.

Matar da ta taimaki harkar ilimin Najeriya ta rasu

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

A wani rahoton, kun ji cewa Matar da ta kafa makarantar mata ta Vivian Fowler Memorial. College a jihar Legas, Misis Leila Fowler ta riga mu gidan gaskiya.

Makarantar da marigayiyar ta kafa ce ta tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, 7 ga watan Satumba, 2025.

Saboda rawar da ta taka wajen ilimi da ci gaban al’umma, marigayi Oba Adeyinka Oyekan II ya karrama ta da sarautar Yeye Mofin na Legas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262