Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Katsina, an Tura Tsageru zuwa Barzahu
- Dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da yin artabu da 'yan ta'adda don kokarin samar da zaman lafiya a sassa daban-daban na kasar nan
- Sojojin sun yi arangama da wasu 'yan ta'adda a jihar Katsina, inda suka samu nasarar hallaka fiye da guda 20
- Hakazalika, sun kuma samu nasarar kubutar da mutanen da aka sace wadanda suka hada da mata da kananan yara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda 23, a jihar Katsina.
Dakarin sojojin sun samu nasarar ne yayin artabun da suka yi da 'yan ta'adda a karamar hukumar Kankara.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma, sun kaddamar da babban farmaki a ranar 6 ga watan Satumba a kauyen Pauwa da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
Dakarun sun yi arangama da ’yan ta’adda a kan Dutsen Pauwa, inda aka yi musayar wuta mai zafi.
"A yayin fafatawar, an kashe ’yan ta’adda 23, sannan aka ceto mata 12 da yara 11 da ake tsare da su."
"Dakarun sun kuma kwace babura guda biyar, kayan gyara, kayan abinci da wasu kayayyaki waɗanda aka lalata a wurin."
- Wata majiya
Dakarun Sojoji sun ceto mutane
Hakazalika Dakarun sojoji da ke sintiri a karamar Hukumar Matazu ta jihar Katsina sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su.
Sojojin sun ceto mutanen ne bayan sun fafata da ’yan ta’adda a kusa da kauyen Shaiskawa.
Majiyoyin sun nanata aniyar rundunar sojojin Najeriya na tabbatar da samar da yanayi mai tsaro domin inganta harkokin noma da sauran ayyukan tattalin arziki.

Source: Twitter
Iyalan 'yan ISWAP sun mika wuya
Haka kuma, wasu iyalai na ’yan ta’addan ISWAP/JAS, waɗanda suka haɗa da mata biyu da yara biyu, sun miƙa wuya ga dakarun bataliya ta 192 a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Kara karanta wannan
Sojojin sama sun yi ruwan bama bamai kan mayakan Boko Haram, an soye 'yan ta'adda
Binciken farko ya nuna cewa sun tsere ne daga kauyen Lekshe, kuma ana ci gaba da yi musu tambayoyi.
Karanta wasu labaran kan sojoji
- Sojojin sama sun yi ruwan bama bamai kan mayakan Boko Haram, an soye 'yan ta'adda
- Sojoji sun yi barin wuta, an kashe 'yan ta'adda, an kwato kayan hada bama bamai
- Dakarun sojoji sun toshe kofofin tsira ga 'yan ta'addan Boko Haram, an kashe miyagu
- 'Yan bindiga sun sha wuta hannun sojojin sama, sun sako mutanen da suka sace a Zamfara
Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan tantiran 'yan bindiga a jihar Katsina.
Sojojin sun samu nasarar dakile wani harin da 'yan bindiga suka kai da nufin yin awon gaba da matafiya a kan titin hanyar Funtua zuwa Gusau.
Hakazalika, dakarun sojojin sun yi nasarar kubutar da mutanen da 'yan bindigan suka yi yunkurin sacewa, wadanda ke cikin wasu motoci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
