Lokaci Ya Yi: Matar da Ta ba Harkar Ilimi Gagarumin Gudummuwa a Najeriya Ta Rasu
- Matar da ta kafa makarantar mata ta Vivian Fowler Memorial College a jihar Legas, Misis Leila Fowler ta riga mu gidan gaskiya
- Marigayiyar na daya daga cikin matan da ake ganin sun bai wa harkar ilimi gudummuwa mai girma musamman wanda ya shafi mata
- Makarantar Vivian Fowler Memorial College ta yi alhinin wannan rashi, inda ta bayyana Leila Fowler a matsayin mace mai hangen nesa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Misis Leila Fowler, mai rike da sarautar Yeye Mofin ta Legas, kuma wacce ta kafa makarantar mata ta Vivian Fowler Memorial College for Girls, ta riga mu gidan gaskiya.
Makarantar da marigayiyar ta kafa ce ta tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, ta ce Leila Fowler ta mutu tana da shekaru 91 a duniya.

Source: Facebook
An tabbatar da mutuwar Leila Fowler
Jaridar The Cable ta tattaro cewa marigayiyar na daya daga cikin matan da ake ganin sun bai wa harkokin ilimi gudummuwa a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
"Cikin bakin ciki muke sanar da rasuwar mahaifiyarmu kuma shugabarmu, Leila Fowler.
"Ta kasance mace mai hangen nesa, kwararriya a harkar shari’a, kuma mai kishin ilimi, wacce ta kafa makarantar Vivian Fowler Memorial College for Girls don karfafa ilimin mata.”
Takaitaccen bayani kan rayuwar Misis Leila
An haifi Leila Fowler a jihar Legas a ranar 23 ga Maris, 1933. Ta yi karatu a CMS Girls’ School, Legas da kuma Queen of the Rosary College, Onitsha, inda ta samu shaidar gama sakandire a 1951.
Ta fara aikinta a matsayin malamar makaranta, daga bisani ta yi karatun jinya a St Thomas’ Hospital, Landan. Daga nan ta shiga makarantar shari’a ta Middle Temple, ta zama lauya a 1962.

Kara karanta wannan
Tinubu ya waiwayi daliban da aka sace lokacin Jonathan, ya ba su tallafin N1.85bn
Leila Fowler ta yi fice a fannin harkokin shari’a, musamman kan dokar inshora kuma ta yi aiki a matsayin lauya mai zaman kanta.
Haka kuma ta taka rawa a kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA), Red Cross, da Corona Schools Trust Council.
Burinta na bayar da gudummuwa wajen bunkasa harkokin ilimi ne ya sa ta kafa makarantar Vivian Fowler Memorial College for Girls, wacce ta shahara a jihar Legas.

Source: Facebook
Yadda aka nada ta sarauta a jihar Legas
Leila Fowler ta kasance matar marigayi Farfesa Vidal Fowler, likita kuma masanin kimiyya, har zuwa rasuwarsa a 2015.
Saboda rawar da ta taka wajen ilimi da ci gaban al’umma, marigayi Oba Adeyinka Oyekan II ya karrama ta da sarautar Yeye Mofin na Legas.
Makarantar ta bayyana marigayiyar a matsayin mai kishin addini, mai taimakon al’umma, kuma mai sha’awar kiɗe-kide a rayuwarta, Leadership ta ruwaito.
Shugaban FCTA ta farko a Abuja ta mutu
A wani rahoton, kun ji cewa matar da ta fara zama shugabar ma'aikatan hukumar FCTA a mulkin Bola Tinubu, Grace Adayilo ta mutu.
Wata majiya daga hukumar raya birnin tarayya (FCTA), ta tabbatar da cewa Grace ta mutu ne a safiyar ranar Litinin, 1 ga Satumbar 2025.
Mutuwar Grace Adayilo ta girgiza Abuja, da kasar, kasancewar ita ce mace ta farko, kuma 'yar asalin birnin tarayya da ta rike shugabancin FCTA.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

