NUPENG da Dangote: Ana Rikicin da ke Shirin Girgiza Harkar Fetur a Najeriya
- NUPENG ta yi barazanar shiga yajin aiki bisa zargin cewa Aliko Dangote na neman kwace raba su da dakon mai
- Kungiyoyin NUGASA da AROGMA sun raba ra’ayi, yayin da IPMAN ta nemi a sasanta rikicin cikin lumana
- Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani domin hana yajin aiki da kauce wa jefa talakawa cikin tsadar man fetur
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rikici ya kunno kai tsakanin kungiyar masu dakon mai ta NUPENG da matatar Dangote kan batun jigilar mai zuwa gidajen man fetur.
Kungiyar NUPENG ta yi barazanar shiga yajin aiki bayan zargin Dangote da keta dokokin ƙwadago da kuma neman raba direbobin tankar mai da aikin su.

Source: Getty Images
Rahoton BBC ya nuna cewa Ministan kwadago na Najeriya yana tattaunawa da shugabannin NUPENG da kuma jami’an kamfanin Dangote domin samo mafita ga wannan kiki-kaka.
Barazanar da kungiyar NUPENG ta yi a Najeriya
Shugabannin NUPENG sun bayyana cewa matakin Dangote zai jefa dubban direbobin manyan motoci cikin rashin aikin yi, wanda hakan zai yi tasiri kai tsaye ga daruruwan iyalai a fadin ƙasar.
Mataimakin shugaban kungiyar direbobin tankar mai ta PTD, Lawan Garba, ya ce doka ba ta bai wa wani kamfani damar tara mai daga matatar sa sannan ya rarraba shi kai tsaye ba.
Ya jaddada cewa direbobi sama da 30,000 na iya rasa aikin su idan aka ci gaba da wannan tsari, lamarin da zai iya jawo tsaikon zirga-zirgar tankuna a ƙasar.
Kungiyar NUGASA ta ce na tare da NUPENG
Ƙungiyar masu gidajen mai da iskar gas ta kasa (NUGASA) ta nuna cikakken goyon baya ga NUPENG a rikicin.
Mataimakin shugaban ƙungiyar, Abdullahi Idris, ya ce matakin Dangote tamkar kora ce ga masu gidajen mai da direbobi da suka shafe shekaru suna gudanar da harkar man fetur.
A cewarsa, idan Dangote zai rika kai fetur gidajen mai da kansa, to sauran masu rarrabawa za su rasa aikin yi.
IPMAN ta nemi a sasanta da kamfanin Dangote
A gefe guda kuma, kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta yi kira da a sassauta rikicin cikin lumana.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Abubakar Mai Gamji Shettima, ya bukaci dukkan ɓangarorin da su zauna a teburin tattaunawa tare da Dangote domin kauce wa jefa talakawa cikin wahala.
Ya ce mafi muhimmanci shi ne a samu mafita mai dorewa da za ta tabbatar da wadatar mai ba tare da tashin farashi ba.

Source: Getty Images
AROGMA ta goyi bayan Dangote
A daya bangaren, kungiyar masu gidajen mai da iskar gas (AROGMA) ta bayyana goyon bayanta ga matatar Dangote.
Shugaban ƙungiyar, Bashir Ɗanmalam, ya ce lokaci ya yi da za a dakatar da NUPENG daga amfani da karfinta wajen tilastawa talakawa biyan karin kudin mai.
Ya kuma bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa akwai isasshen man fetur da zai wadatar da ƙasar har na tsawon wata guda.
Matakin gwamnatin tarayya a rikicin
Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani tare da roƙon NUPENG da ta dakatar da shirin shiga yajin aiki, tana mai tabbatar da cewa ana tattaunawa da Dangote domin warware rikicin.
Punch ta wallafa cewa Ministan kwadago ya sha alwashin cewa gwamnati ba za ta yi shiru ba kan duk wani abu da zai iya jefa al’umma cikin tsadar rayuwa.
Harajin fetur zai shafi 'yan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa a shekarar 2026 ne ake saka ran gwamnatin za ta fara karbar harajin 5% na man fetur.
Rahotanni sun nuna cewa harajin zai jawo karin kudin mai a fadin kasa kuma hakan zai shafi rayuwar 'yan Najeriya.
Legit ta rahoto cewa matakin zai kara kudin da 'yan acaba za su rika kashewa tare da jawo karin kudin hawa jirgin sama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


