Uwargidan Gwamna Ta Kafa Tarihi a Kasar Hausa da Aka Nada Ta Sarauta a Jihar Katsina

Uwargidan Gwamna Ta Kafa Tarihi a Kasar Hausa da Aka Nada Ta Sarauta a Jihar Katsina

  • Mai martaba Sarkin Daura da ke jihar Katsina ya nada Hajiya Zulaihat Dikko Radda a matsayin Jagaban Matan Hausa
  • Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda tare da shugaban APC na jihar da wasu sarakuna sun halarci bikin wannan nadi a fadar Sarkin Daura
  • Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar Faruq ya ce ya nada Hajiya Zulaihat ne saboda irin gudummuwar da take bai wa mata ta hanyar tallafa masu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Uwargidan mai girma gwamnan jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Umaru Radda ta zama ta farko da aka bai wa sarautar Jagaban Matan Hausa.

Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Faruq Umar Faruq, shi ne ya naɗa uwargidan gwamna, Hajiya Zulaihat Dikko Radda, a wannan sarauta.

Hajiya Zulaihat Dikko Radda.
Hoton uwargidan gwamnan Katsina, Hajiya Zulaihat a wurin nada ta Jagaban Matan Hausa Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Babban sakataren watsa labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta taba sarakuna, Wamban Dawakin Zazzau ya rasu a gadon asibiti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da wannan gagarumin bikin nadin ne a fadar Sarkin Daura, jim kaɗan bayan Hawan Magajiya da aka fi sani da Sallar Gani.

Gwamna Dikko Radda ya halarci bikin nadi

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya samu halartar wannan taro tare da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Sani Aliyu Daura.

Haka zalika mata masu rike da sarautun gargajiya daban-daban sun halarci wannan bikin nadi a fadar Sarkin Daura domin nuna goyon baya ga mai dakin Dikko.

Mai martaba Sarkin Daura ya mika takardar naɗin da kuma lullube uwargidan gwamnan da kayan al’ada a wurin wannan gagarumin biki.

Dalilin ba uwargidan gwamnan Katsina sarauta

Da yake jawabi, Sarkin ya bayyana cewa an ba Hajiya Zulaihat wannan sarauta ne saboda jajircewarta wajen tallafawa mata musamman a bangaren ƙarfafa su da abubuwan raya tattalin arziki.

Alhaji Faruq Umar ya bayyana wannan sarauta a matsayin ta farko da aka baiwa uwargidan gwamna, inda ya yaba da kokarinta ba wai ga mata kaɗai ba, har da maza.

Kara karanta wannan

Sarauniyar kasar Hausa ta kafa tarihi a hawan sallar gani da aka yi a Daura

"Sarautar Jagaban Matan Ƙasar Hausa ta kasance wata babbar girmamawa da ta nuna rawar da uwargidan gwamnan Katsina take taka wa wajen ci gaban al’umma da ƙarfafa mata a jihar," in ji sanarwar
Hajiya Zulaihar Dikko Radda.
Hoton lokacin da Sarkin Daura ya mika takardar nadi ga uwargidan gwamnan Katsina a gaban mijinta Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Taron ya ja hankali manyan mutane inda masu rike da sarautun gargajiya daga sassa daban-daban suka halarci fadar Sarkin Daura domin nadin Hajiya Zulaihat.

Mahalarta taron sun kuma nuna goyon baya da yabo ga sabuwar Jagaban Matan Kasar Hausa, Hajiya Zulaihat Dikko Umaru Radda, in ji rahoton Premium Times.

Hadimin uwargidan gwamna ya yi karin haske

Legit Hausa ta zanta da Mu'azu Shamsudeen Dalhatu, shugaban gidauniyar da uwargidan gwamnan Katsina ke tallafawa al'umma a bangaorori daban-daban na rayuwa.

Shamsudeen ya nuna farin cikinsa bisa wannan nadi da Sarkin Daura ya yi Hajiya Zulaihat, in da ya ce matar gwamnan Katsina ta cancanci wannan sarauta.

Da yake bayyana wasu daga cikin ayyukan da gidauniyar matar gwamnan ke yi a fadin jihar Katsina, Shamsu ya ce:

"Da farko ina godiya ga Allah, sannan muna godewa mai martaba bisa wannan karrama wa, na san ya bai wa Hajiya wannan sarauta ne saboda ayyukan da take yi na tallafa wa marasa karfi."

Kara karanta wannan

'Sau 2 ba mu sallar Juma'a': Musulmai sun roki sauya ranar nadin Sarki da za a yi

"A gidauniyarta, ta ba mu dama mu nemi marasa karfi da ke bukatar taimako a fannin lafiya da karatu, kuma na san cewa an tallafawa mutane da dama."

Yadda matar gwamna ke taimakon mata

Hadimin matar gwamnan ya bayyana ayyuka da yawa da Jagaban Matan Hausa take yi, daga ciki ya ambaci wani shiri na tallafawa mata da jari don su dogara da kansu.

"Hajiya ta kirkiro wani shiri da aka zakulo mata sama da 200 aka ba su jari, wasu daga ciki sun samu N200,000. Wannan al'amari ne mai girma da zai taimaka masu wajen bunkasa kasuwancinsu," in shi.

Ya ce wadannan da ma wasu ayyukan da lokaci ba zai ba da damar a ambata ba sune dalilan da mai martaba ya ga dacewar ba Hajiya Zulaihat wannan sarauta.

Gwamna Radda ya ziyarci kabarin Buhari

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kai ziyara ta musamman kabarin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Gwamnan ya kai wannan ziyara ne a lokacin da ya halarci bikin Hawan.Magajiya na sallar Gani, babbar al’ada a masarautar Daura da ke Katsina.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa aka sake fasalin kabarin Buhari a Daura'

Radda ya samu rakiyar wasu daga cikin mukarrabansa, suka yi addu’o’i domin neman rahamar Allah ga marigayin, tare da fatan Allah ya gafarta masa kura-kuransa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262