An Fara kai Ziyara Kabarin Buhari, Gwamna Dikko Radda da Tawaga Sun Je Daura

An Fara kai Ziyara Kabarin Buhari, Gwamna Dikko Radda da Tawaga Sun Je Daura

  • Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya kai ziyara gidan marigayi Muhammadu Buhari a Daura, inda ya yi addu’ar neman rahama gare shi
  • Ziyarar ta zo ne a lokacin da gwamnan ya halarci bikin Hawan Magajiya na sallar Gani, babban al’ada a masarautar Daura
  • Bayan ziyarar, gwamna Dikko Radda ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da girmama addini da al’ada tare da hada kan al’ummar jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kai ziyara ta musamman kabarin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A ranar 13 ga Afrilun 2025 shugaba Muhammadu Buhari ya rasu a wani asibitin London yana da shekaru 82.

Gwamna Radda da tawagarsa na yi wa Buhari addu'a
Gwamna Radda da tawagarsa na yi wa Buhari addu'a. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ziyayar da Dikko Radda ya kai ne a cikin wani sako da Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Kano ya gana da Sheikh Jingir kan rasuwar malamin Izala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Radda ya ziyarci kabarin Buhari a Daura

Gwamnan ya samu rakiyar wasu daga cikin mukarrabansa, suka yi addu’o’i domin neman rahamar Allah ga marigayin, tare da fatan Allah ya gafarta masa kurakuransa.

Haka kuma, ya yi addu’ar samun zaman lafiya da hadin kai ga Katsina da Najeriya gaba ɗaya, yana mai kira da a ci gaba da gina al’umma.

An yi hawan Hawan Magajiya a garin Daura

Premium Times ta wallafa cewa ziyarar ta kasance cikin jerin ayyukan Gwamna Radda a Daura, inda ya halarci bikin Hawan Magajiya na sallar Gani.

Bikin ya kasance wani muhimmin taron addini da al’adu da masarautar Daura ke gudanarwa duk shekara domin tunawa da haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).

Radda ya ce bikin na da muhimmanci wajen hada al’umma wuri guda domin nishadi, addu’a da tunatarwa, tare da ci gaba da dorewar al’adun da masarauta ke alfahari da su tsawon shekaru.

Wasu bayanai game da Marigayi Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

'Abubuwa 4 ne ke rura wutar ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya nemo mafita ga Arewa

Marigayi Muhammadu Buhari ya kasance shugaban da ya yi mulkin Najeriya tsakanin 2015 zuwa 2023 karkashin jam’iyyar APC.

A yayin ziyarar, Dikko Radda ya yi addu’ar Allah ya ji kansa, ya ba masu mulki ikon bin sahun nagartattun shugabanni.

Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu a London yana da shekaru 82, bayan jinya da ya yi bayan sauka daga mulki da shekara biyu.

Mutuwarsa ta bar gibi mai girma a siyasar Najeriya, musamman a jam’iyyar APC da kuma tsakanin al’ummar Arewa.

Lokacin da aka kawo gawar Buhari Najeriya daga London
Lokacin da aka kawo gawar Buhari Najeriya daga London. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Kiran Gwamna Radda ga mutanen Katsina

Gwamna Radda ya yi kira ga al’ummar Katsina da Najeriya baki ɗaya da su ci gaba da yin addu’a domin samun zaman lafiya da wadata.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da mutunta darajar addini, al’ada domin bunkasa ci gaban jihar da dorewar hadin kan al’umma.

An yi auren jikar Buhari a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa an daura auren jikar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna.

Legit Hausa ta rahoto cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayar da auren a wani masallaci a Kaduna.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Sanata Shettima ya dura Kaduna wajen auren ne domin girmama marigayi shugaba Buhari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng