Tubabbun 'Yan Bindiga Sun Dawo Shiga Jama'a, Kasuwa da Asibiti a Kaduna
- Gwamnatin Kaduna ta kulla yarjejeniya da shugabannin ‘yan bindiga, wacce ta ba su damar shiga kasuwanni da asibitoci
- Yarjejeniyar ta kawo sauyi a yankin Birnin Gwari, inda jama’a ke jin sassauci bayan shekaru na fargaba da satar mutane
- Shugabannin al’umma sun ce zaman lafiya ya dawo, sai dai suna kira da a ci gaba da kiyaye yarjejeniyar domin dorewar alkawarin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Bayan wata shida na tattaunawa, gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta kammala yarjejeniyar zaman lafiya da jagororin ‘yan bindiga.
Yarjejeniyar da aka fara aiwatarwa kusan watanni goma da suka gabata ta kawo kwanciyar hankali ga Birnin Gwari da kewaye.

Source: Facebook
Wani bidiyo da tasahar AIT ta wallafa a X ya nuna yadda jama'a ke walwala a Birnin Gwari bayan sulhun da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan mataki ya kawo sauyi ga al’umma da suka dade cikin tsoro da hijira sakamakon hare-haren satar mutane da garkuwa da su, da kuma karbar haraji daga manoma da makiyaya.
Rahotanni sun nuna cewa, yarjejeniyar ta bai wa tsofaffin ‘yan bindiga damar shiga kasuwanni da asibiti cikin kwanciyar hankali, a madadin su daina satar mutane, karbar haraji ko lalata gonaki.
An yaba da samun zaman lafiya a Kaduna
A wani taron masu ruwa da tsaki a da aka yi, Hakimin Kuyello, Alhaji Yusuf Abubakar, ya ce yankin nasa ya samu zaman lafiya tsakanin Fulani da Hausawa.
Sai dai duk da haka, ya nuna damuwa kan sauran al’amuran ta’addanci da ba a kawar gaba ɗaya ba.
Kokarin da Gwamnatin jihar Kaduna ta yi
A nasa jawabin, shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Malam Sani Kila, ya bayyana farin ciki da dawowar zaman lafiya a Birnin Gwari.
Ya ce cunkoson abubuwan hawa da ake gani a tituna na nuni da cewa al’amura sun fara dawowa daidai.
Kila ya jaddada cewa gwamnatin Kaduna ta kafa kwamitin tattaunawa na musamman domin gina amincewa tsakanin jama’a da tabbatar da dorewar zaman lafiya.
Rahoton tashar Arise ya tabbatar da cewa Kila ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da cika alkawuran da ta dauka cikin yarjejeniyar.
Rawar da masarautar Birnin Gwari ta taka
Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubair Jibril MaiGwari II, ya ce yarjejeniyar ta dauki wata shida kafin ta kammala, kuma yanzu haka ta kawo zaman lafiya.
Ya ce wannan nasara ta samo asali ne daga hadin kan dukkan bangarorin da abin ya shafa, inda ya bukaci a ci gaba da kiyaye nasarar da aka samu.
Wakilin tsofaffin ‘yan bindiga a yankin, Abubakar Uban Jambrose, ya yaba da kokarin Gwamna Uba Sani.
Dalilin sulhu da 'yan bindiga a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kaduna, ya bayyana cewa suna sulhu da 'yan bindiga ne domin kawo karshen zubar da jini.
Gwamnan ya ce yaki da bindiga da bama bamai kadai ba za su kawo karshen matsalar 'yan ta'adda ba.
Uba Sani ya yi magana ne yayin wani taro da kungiyar Izala karkashin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta shirya a Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

