NLC Ta Taso da Batun Mafi Karancin Albashi, Ta Yi Barazana ga Tinubu

NLC Ta Taso da Batun Mafi Karancin Albashi, Ta Yi Barazana ga Tinubu

  • Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta koka kan mafi karancin albashin N70,000 da ake biyan ma'aikata a Najeriya
  • NLC ta bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta duba halin kuncin da ma'aikata suka tsinci kansu a ciki
  • Ta kuma tabo batun maganar tsunduma cikin yajin aiki idan ba a biya musu bukatun da su ka nema

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ƙungiyar Ƙwadago ta kasa (NLC) ta sake tabo batun maganar mafi karancin albashi.

Kungiyar NLC ta bukaci a sake duba mafi karancin albashi na kasa domin a kara yawansa, tana mai cewa N70,000 ta yi kadan a halin da ake ciki a yanzu.

NLC na son a kara mafi karancin albashi
Hoton Shugaba Bola Tinubu da na shugabannin kungiyoyin kwadago Hoto: @DOlusegun, @NLCHeadquarters
Source: Facebook

Babban sakataren rikon kwarya na NLC, Benson Upah, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

"A koresu": Kungiyar 'yan Arewa ta ba Tinubu shawara kan rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kiran na NLC ya biyo bayan matakin da wasu jihohi suka dauka na kara albashi a baya-bayan nan.

A watan Yulin 2024, Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi, inda aka kara albashin daga N30,000 zuwa N70,000 ga ma’aikatan gwamnatin tarayya, jihohi da kuma masu zaman kansu.

Sai dai hauhawar farashin kayayyaki da karuwar kuɗin abinci, sufuri, haya da wutar lantarki ya lalata darajar wannan albashi.

NLC na son a karawa ma'aikata albashi

Babban sakataren na kungiyar NLC ya bayyana cewa ma’aikata na fama da tsananin wahala wajen rayuwa.

"Gaskiya ita ce, N70,000 ba za ta tabuka komai a wannan halin matsin tattalin arzikin ba. Ma’aikata na fama da matsi mai tsanani, kuma idan gwamnati ba ta yi gaggawar ɗaukar mataki ba, rikicin neman tsira daga yunwa da talauci zai kara ta’azzara."

- Benson Upah

NLC na iya shiga yajin aiki

Kara karanta wannan

Jerin jihohin da mafi karancin albashi ya kusa N100,000 ko sama da haka a Najeriya

Ya kara da cewa, ko da yake NLC na goyon bayan tattaunawa, har yanzu yiwuwar shiga yajin aiki na nan muddin gwamnatin tarayya ta kasa ɗaukar matakin da ya dace, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Haka kuma, shugaban kungiyar manyan ma’aikatan gwamnatin Najeriya (ASCSN), Shehu Mohammed, ya yaba wa jihohin da suka kara albashi, yana mai cewa hakan ya zama darasi a fili ga gwamnatin tarayya.

“Tun daga farko a lokacin tattaunawa, bukatar mu ita ce a bayar da albashin da zai iya ciyar da ma’aikaci da iyalansa. Mun gabatar da N250,000 a matsayin abin da ya fi dacewa."
“Mu gayawa kanmu gaskiya. Idan mutum ya biya kuɗin wuta daga N70,000, abin da zai ragu ba zai iya ɗaukar iyali sama da kwana 10 ba."

- Shehu Mohammed

NLC ta yi kira ga gwamnati kan mafi karancin albashi
Hoton shugaban NLC, Joe Ajaero, yayin wata zanga-zanga Hoto: @NLCHeadquarters
Source: Facebook

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta haɗa da ƙarin albashi manufofi da za su rage tsadar rayuwa, ciki har da samar da gidaje masu sauƙi, kula da lafiya da sufuri mai rangwamen farashi.

Wani malamin makaranta a Katsina, Shafi'u Halliru, ya shaidawa Legit Hausa cewa albashin da ake biyan ma'aikata ya yi kadan.

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

"Wannan mafi karancin albashin suna kawai ya tara don ya yi kadan. Yadda rayuwa ta yi tsada babu inda kudin su ke zuwa."
"Babu yadda za a yi ya biyawa ma'aikaci dukkani bukatun da yake da su a wata. Maganar gaskiya ya kamata a kara yawan abin da ake biya."

- Shafiu Halliru

Gwamnan Imo ya kara albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya karawa ma'aikata mafi karancin albashi.

Gwamna Hope Uzodinma ya kara mafi karancin albashi daga N76,000 zuwa N104,000 ga ma'aikata.

Hakazalika, Gwamna Uzodinma ya maida mafi karancin albashin likitoci zuwa N503,000 a kowane wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng