'Abubuwa 4 ne Ke Rura Wutar Ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya Nemo Mafita ga Arewa

'Abubuwa 4 ne Ke Rura Wutar Ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya Nemo Mafita ga Arewa

  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa talauci da rashin aiki na matasa su ne tushen ta’addanci a yankin Arewacin Najeriya
  • Ya gargadi shugabanni da su daina yaudara da siyasantar da batun tsaro ta hanyar kiran luguden bama-bamai a kan yan ta’adda
  • Sani ya ce dole ne shugabanni su ɗauki alhakin kare jama’a, tare da inganta makarantu, asibitoci da kasuwanci a yankunan karkara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna – Gwamnan Uba Sani, ya ce talauci, jahilci, rashin aikin yi da watsi da yankunan karkara su ne tushen matsalar rashin tsaro a yankin Arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa babu isassun makarantu, asibitoci da kasuwanni a karkara, wanda ya ba yan bindiga damar amfani da talaucin jama’a wajen jawo su zuwa aikata laifuffuka.

Gwamna Uba Sani ya ce talauci, jahilci, rashin aiki ne ke rura wutar ta'addanci a Arewa
Gwamna Uba Sani, yana jawabi a wani taro da aka shirya kan tsaro a Kaduna. Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Abubuwan da ke rura ta'addanci a Arewa

Kara karanta wannan

"Mun gano tushen matsalar": Gwamna Uba Sani ya fadi dalilin sulhu da 'yan bindiga

Gwamnan jihar na Kaduna ya fadi hakan ne a wajen gabatar da wani littafi mai suna ''Matsaya ta,'' wanda marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya rubuta, kuma Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara shi zuwa Larabci, inji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shawarci ‘yan adawa da su daina siyasantar da batun tsaro ta hanyar ikirarin cewa za a iya murkushe ‘yan bindiga da makamai kawai.

Uba Sani ya ce rashin tsaro a Arewa maso Yamma ya bambanta da na Boko Haram a Arewa maso Gabas, wanda ke da manufa, yana mai cewa talauci, rashin aikin yi da watsi da al’ummomin karkara sune tushen 'yan bindiga.

'A cire siyasa a harkar tsaro' - Uba Sani

Gwamnan ya ce “ba za a iya magance rashin tsaro da amfani da bindigogi kaɗai ba,” yana mai cewa, duk wanda ke ikirarin kawo karshen ta'addanci da bindiga, yana siyasa ne kawai.

Ya ce:

“Dole ne mu ji tsoron Allah, mu daina yaudarar mutane domin wannan hanyar ba za ta yi aiki ba."

Gwamna Sani ya lura cewa adadin jami’an tsaro a Najeriya ya ragu duk da yawan karuwar al’ummar kasar a cikin shekaru 45 da suka gabata.

Kara karanta wannan

"Yaudara ce": Gwamna Uba Sani ya fallasa 'yan siyasa kan matsalar rashin tsaro

"A cikin 1970, bayan yakin basasa, Najeriya tana da sojoji kusan 300,000, amma a yau ba su kai 250,000 ba, yayin da yawan al'ummarmu ya karu da sama da miliyan 100. Ta yaya wani zai ce bindigogi kaɗai za su magance matsalar? Ba zai yiwu ba."

- Gwamna Uba Sani.

Gwamna Uba Sani ya ce sai an yi amfani da wasu hanyoyi da ba na makamai ba don magance matsalar tsaro.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani yana jawabi a wani taro. Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Rashi jami'an tsaro a jihohin Arewa

Jaridar Punch ta rahoto Gwamna Uba Sani ya kuma nuna matukar damuwa game da rashin jami’an tsaro a manyan sassan Arewa maso Yamma, inda ya ce:

“Idan ka yi tafiya zuwa Zamfara, Birnin Gwari, ko dazuzzukan Katsina, za ka iya yin tafiyar kilomita 50 ba tare da ka ga jami’in ‘yan sanda ba, balle sojoji. Muna da manyan yankuna a wannan kasa ba tare da jami'an tsaro ba."

Ya ce garuruwan da hare-hare suka shafa ne suka yanke shawarar yin sulhu da 'yan bindiga, bisa shawarwarin shugabanninsu da malamai, kuma sun ga fa'idar yin haka.

Da yake kawo misali da Birnin Gwari, Uba Sani ya bayyana cewa basaraken yankin ne ya jagoranci dawo da zaman lafiya a yankin.

Rashin magance matsalar tsaro a Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mai girma gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi jihar.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fasa kwai, ya fallasa yadda 'yan majalisa ke 'satar kudaden jama'a'

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa idan da yana da iko da jami’an tsaro, da zai iya warware matsalar tsaro cikin mako biyu kacal.

Gwamnan ya ce ya san inda ’yan bindiga ke buya a jihar, yana bibiyar motsinsu a wayarsa, yana mai cewa wannan babbar matsala ce da ke damun jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com