Obi Ya Sha Kunya a Gida, Daruruwan Mutane Sun Kunyata Shi da El Rufai a Coci
- Daruruwan masu zanga-zanga sun yi wa Peter Obi ihu a Owerri da ke jihar Imo bayan wata ziyara
- Hakan ya zo ne saboda Obi ya kawo tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wurin taron Katolika
- Masu zanga-zangar sun kira El-Rufai makiyi na Igbo da Kiristoci, suna cewa mulkinsa a Kaduna ya jawo kisan mutane
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Owerri, Imo - Daruruwan masu zanga-zanga sun yi wa tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ihu a Owerri.
Masu zanga-zangar sun yi haka ne saboda gayyatar Mallam Nasir El-Rufai zuwa jihar Imo da ke Kudu.

Source: Twitter
Abin da ya faru da Obi, El-Rufai a Imo
Dukkan shugabannin adawa biyu sun halarci taro na Odenigbo da Katolikan Owerri suka shirya, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’ar gari inda ake ganin El-Rufai a matsayin makiyi.
El-Rufai ya sauka a Imo ranar Juma’a, inda aka karɓe shi a fadar Eze Agumanu na Nekede, kafin zuwa wajen taron Katolika.
Kasancewarsa a taron addini tare da Obi ta fusata mutane, inda suka fara raira wakoki suna cewa Peter Obi ya kawo makiyi.
Masu zanga-zangar sun yi zarge-zargen cewa El-Rufai ya nuna ƙiyayya da Igbo da Kiristoci, kuma mulkinsa a Kaduna ya jawo zubar jini.
Wasu daga cikin allunan zanga-zangar sun nuna rubuce-rubuce irin su “Ka daina yaudararmu, Peter Obi, El-Rufai makiyi ne.”
Dakarun tsaro sun hana masu zanga-zangar hana Obi da El-Rufai shiga harabar, inda aka gudanar da babban taron.
Wasu suka bayyana takaici kan Obi saboda kusantar wanda suka kira makiyi, suna cewa hakan ya sa ba za su girmama shi ba.
Sun ce:
“Girmamawarmu ga Obi ta gushe yau, da ya bayyana da makiyin Igbo, shi ma ya zama makiyi a wurinmu.”

Source: Twitter
Obi, El-Rufai sun gana da shugabannin ADC
Haka kuma wasu shugabannin SDP sun yi zanga-zanga kan taron da El-Rufai ke shirin yi a jihar kafin wannan taron Katolika.
Jagororin jam'iyyar ADC na ƙasa, ciki har da Obi da El-Rufai, sun gana da shugabannin ADC na Imo a gidajen magabatan siyasa.
Wadanda suka halarta sun haɗa da Farfesa Batos Nwadike, Cif Mike Nwachukwu, Rt. Hon. Maduagwu, da wasu sarakunan gargajiya na jihar Imo.
Ya kara da cewa, daga Enugu ya wuce Owerri don cin abincin dare da aka shirya a girmama tsohon gwamna, Nasir El-Rufai.
An ƙaryata shigar El-Rufai coci saboda Tinubu
Kun ji cewa an yi ta yada wasu hotuna sun nuna Malam Nasir El-Rufai a coci, inda aka ce yana kokarin jawo limamai don zaben 2027.
El-Rufai ya halarci jana’izar tsohon kwamishinan Anambra, Mathias Anohu ne, ba wai ya je neman goyon bayan Fastoci ba.
An tabbatar da cewa hoton daga jana’iza ne da aka gudanar a Okija, kuma El-Rufai ya wallafa hakan da kansa a kafar sadarwa.
Asali: Legit.ng

