An Sake Taso Tinubu a Gaba kan Cafke Shugaban Falsɗinawa, an 'Gano' Makirci a Ciki
- Bayan cafke shugaban Falsɗinawa a birnin Abuja da ke Najeriya, ana ci gaba da matsawa gwamnati lamba
- Kungiyar Musulmi ta Al-Harakatul-Islamiyyah ta bukaci a saki Ramzy Abu Ibrahimda aka tsare ba tare da sharadi ba
- Shugaban kungiyar, Mallam Abdur-Razzaq Al-Ameen, ya ce kama shi da aka yi ya saba doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An taso hukumomin Najeriya a gaba kan cafke shugaban Falsɗinawa a kwanakin baya.
Wata kungiya ta Musulmi ta bukaci a saki ɗan asalin Falasdinu da ke zaune a Najeriya ba tare da sharadi ba bayan kama shi.

Source: Facebook
Cafke Ramzy na kara jawo wa Tinubu magana
Hakan na cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a taron manema labarai a birnin Ilorin na jihar Kwara da Daily Trust ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanda aka kama, Ramzy Abu Ibrahim, ya shafe sama da shekaru 33 yana rayuwa a Najeriya cikin lumana da zaman lafiya.
Kungiyar Al-Harakatul-Islamiyyah ta zargi cewa cafke shi din ya biyo bayan matsin lamba daga Isra’ila karkashin yarjejeniyar tsaro da Najeriya.
Shugaban kungiyar, Mallam Abdur-Razzaq Abdulwahab Al-Ameen Aladodo, ya ce an tilasta tsare shi ne saboda tasirin Isra’ila a yarjejeniyar tsaro tsakanin Najeriya da kasar.
Ya bayyana damuwar kungiyar kan lamarin, yana mai cewa hakan 'ba bisa doka ba ne, rashin tausayi ne kuma abin tayar da hankali' ga Musulmi a Najeriya.
Kungiyar ta ce Ramzy ya rayu cikin lumana shekaru da dama a Najeriya, amma kama shi ya sabawa ikon ƙasar kuma ya nuna halin biyayya ga Isra’ila.

Source: Facebook
Ramzy: Zargin da ake yi wa Tinubu
Kungiyar ta zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da yin hidima ga “masu aikata laifin yaki a Tel Aviv” maimakon ta maida hankali kan matsalolin tsaro a gida.
Al-Ameen ya yi gargadin cewa wannan lamari na iya haifar da rarrabuwar kawunan Musulman Najeriya, wanda ya kira babban haɗari ga gwamnatin Tinubu.
Ya ce:
“Wannan abu na iya zama babban barna ga diflomasiyya da siyasa idan gwamnati ta watsar da muradin Musulmi miliyan 130 a Najeriya saboda Isra’ila.
“Babu bambanci tsakanin ’yan gwagwarmayar Afirka ta Kudu da gwagwarmayar Falasdinawa na kare kansu daga kisan kiyashi da Isra’ila ke yi."
Kungiyar Musulmin ta gode wa ’yan Najeriya da suka nuna adawa da kame shi, tare da kira da a ci gaba da matsin lamba har sai an sakeshi.
Ramzy ya kasance yana jagorantar fafutukar tallafa wa Falasdinawa a Najeriya, musamman wajen bayyana kashe ’yan jarida a Gaza ta hanyar hare-haren Isra’ila.
Farfesa Maqari ya soki kama shugaban Falasɗinawa
Kun ji cewa limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, ya yi Allah-wadai da kama shugaban al’ummar Falasɗinawa a Najeriya.
An ce jami’an da suka bayyana kansu a matsayin rundunar yaƙi da ta’addanci ne suka yi wannan samame a gidan shugaban a Abuja.
Har yanzu ba a bayyana dalilin kama shi ko inda aka kai shi ba, lamarin da ya tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin al’ummarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

