"Yaudara ce": Gwamna Uba Sani Ya Fallasa 'Yan Siyasa kan Matsalar Rashin Tsaro

"Yaudara ce": Gwamna Uba Sani Ya Fallasa 'Yan Siyasa kan Matsalar Rashin Tsaro

  • Matsalar rashin tsaro ta addabi yankin Arewa maso Yamma, inda 'yan bindiga suke cin karensu babu babbaka
  • Mutane da dama na ganin cewa ya kamata a yi amfani da karfi ta hanyar yin ruwan bama-bamai kan 'yan bindigan da ke addabar jama'a
  • Sai dai, Gwamna Uba Sani ya bayyana dalilin da ya sa bin wannan hanyar kadai ba za ta iya kawo karahen matsalar rashin tsaro ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya gargadi ‘yan adawa kan siyasantar da batun matsalar rashin tsaro.

Gwamna Uba Sani ya yi gargadin cewa ikirarin da ke cewa za a iya kare ‘yan bindiga da bama-bamai, yaudara ce kuma rashin gaskiya.

Gwamna Uba Sani ya yi magana kan rashin tsaro
Hotom Gwamna Uba Sani yana jawabi a wajen wani taro Hoto: @Ubasanius
Source: Facebook

Gwamna Uba Sani ya yi wannan magana ne a ranar Asabar yayin kaddamar da littafin “Where I Stand” na marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya kawo tsarin jawo hankalin yara shiga makaranta a Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara littafin zuwa harshen Larabci.

Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ce ta shirya taron a birnin Kaduna.

Gwamna Uba Sani ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a matsayin bako na musamman, tare da kasancewa mai masaukin baki na musamman.

Me Uba Sai yace kan rashin tsaro?

A cewarsa, sabanin ta’addancin Boko Haram a Arewa maso Gabas wanda aka gina bisa akida, rashin tsaron da ya addabi Arewa maso Yamma ya samo asali ne daga talauci, rashin aikin yi da kuma yin watsi da al’ummomin karkara.

"Ba za a iya magance matsalar tsaro ta hanyar amfani da bindigogi kaɗai ba. Duk wanda ya yi irin wannan magana siyasa kawai yake yi."
"Dole mu ji tsoron Allah mu daina yaudarar mutane, domin wannan hanya ba za ta yi tasiri ba."

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya koka kan karancin jami'an tsaro

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin gwamna da ministan tsaro, APC ta fusata kan lamarin

Gwamna Uba Sani ya kuma nuna damuwarsa kan karancin jami'an tsaro a Najeriya duk da yawaitar al’umma cikin sauri.

"A shekarar 1970, bayan yakin basasa, Najeriya tana da sojoji kimanin 300,000. Yau kuma ba su kai 250,000 ba, alhali yawan al’ummarmu ya karu da fiye da miliyan 100."
"To ta yaya wani zai ce bindigogi kaɗai za su magance matsalar tsaro? Ba zai yiwu ba.”

- Gwamna Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya yi maganganu kan rashin tsaro
Hoton gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, yana jawabi a wajen wani taro Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Gwamna Uba Sani ya kuma koka kan rashin isassun jami’an tsaro a yankunan Arewa maso Yamma.

"Idan ka yi tafiya zuwa Zamfara, Birnin Gwari ko dazukan Katsina, za ka iya yin kusan kilomita 50 ba tare da ka haɗu da ɗan sanda ɗaya ba, balle soja."
"Muna da manyan yankuna a wannan ƙasa ba tare da jami’an tsaro ba."

- Gwamna Uba Sani

El-Rufai ya nesanta kansa da Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nesanta kansa da Gwamna Uba Sani.

Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnan wanda ya gaje shi a mulkin jihar Kaduna, ba abokinsa ba ne.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Kirista ya gina masallaci, gwamnan Nasarawa ya yi hudubar juma'a

Tsohon gwamnan ya ba da tabbacin cewa bai yi abota da Uba Sani ba, sai ya dauke shi a matsayin yaronsa wanda ya ba horo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng